Shugaban Kasar Madagascar ya kaddamar da fara amfani da wani tataccen ruwan maganin wani ganye mai kama da sabara ko barbarta, wato Ganyen Madagascar, da ya ce ya na maganin cutar Coronavirus.
Shugaba Andry Rajoelina ya kaddamar da fara amfani da shi, duk kuwa da gargadin da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi cewa babu wani maganin cutar, kuma kuskure ne a yi amfani da maganin gargajiya a ce zai iya warkar da Coronavirus.
Ranar Litinin Cibiyar Sarrafa Magungunan Gargajiya da ke Malagasy, babban birnin Madagascar ta kaddamar da ruwan maganin Madagascar, mai suna Covid-Organics, wanda ya kunshi ganyen Artemisia, mai kama da barbarta, sabara, runhu ko taramniya, wadda kasar ke tinkaho da yalwar sa a tsibirin yankin.
“An gwada Ganyen Madagascar, ya yi aiki ga jikin wadanda aka yi gwajin a kan su, sau biyu kuma sun warke.”
Komawar daliban kasar makarantu ke da wuya, sai gwamnatin Madagascar ta tilasta cewa kowane dalibi sai an yi masa gwajin ingancin maganin Ganyen Madagascar a jikin sa, domin kariya ga cutar Coronavirus.
Shugaban kasar ya bada umarnin a raba wa dalibai da marasa galihu ruwan maganin kyauta, yayin da masu sukuni kuma aka ce da kudin aljihun su za su saya.
Manema labarai a Malagasy sun shaida ganin dandazon jerin gwanon jama’a wadanda aka sa suka bi dogon layi ana diga musu ruwan Ganyen Madagascar a jikin baki.
Ganyen Madagascar Bogi ne – WHO da BBC
Kwana daya bayan fidda rahoton Madagascar, Hukumar Lafiya ta Duniya ta sake nanata matsayar ta, inda ta karyata Madagascar cewa ba gaskiya ba ne, wannan ganye ba ya magani. Sannan kuma ta ja hankali a guji yin gangancin amfani da shi.
Haka BBC ta yi cikakken rahoto a Sashen Turanci, wanda Sashen Hausa ya fasaara a cikin bidiyo, inda ya karyata Ganyen Madagascar.
Discussion about this post