Shugaba Buhari ya garkame Kano na kwanaki 14, ba fita ba shiga

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saka dokar ‘Zaman Gida Dole’ a jihar Kano daga ranar Talata.

Hakan ya biyo bayan matsalolin gwaji da killace mutane da ake fama da su a Kano.

Bayan haka kuma da zargin mace-mace da ake ta yi a Kano na babu-gaira-babu dalili. Sannan kuma ya saka a Yi bincike akai domin sanin gaskiyar abin da ke faruwa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sassauta dokar Hana walwala a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Daga ranar 4 ga watan Mayu, za a ci gaba da walwala tun daga karfe 9 na safe zuwa karfe 8 na dare, inda daga nan kuma za a shiga kulle sai safiyar gobe.

Buhari ya Kara da cewa gwamnati zata mara wa gwamnatin jihar Kano baya domin a kawo karshen matsalolin da suke fama da su da yaki da dakile yaduwar cutar coronavirus.

A dalilin haka Buhari ya ba da umarnin garkame Kano na tsawon kwanaki 14 daga ranar Talata.

Daga nan sai yayi Kira ga gwamnatocin jihohi su ci gaba da samar was mutanen jihohin su lafiya da kuka da al’amuransu domin gujewa kamuwar da Coronavirus.

Share.

game da Author