Sam Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar Bai Fadi Haka Ba! Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkanin kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammad da iyalansa da sahabbansa baki dayan su.

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwa na, masu daraja, ‘yan Najeriya, kamar yadda na san kun gani ko kuma kun ji labari game da wasu miyagun mutane da ke yawo, suna yada wani sharri a kafafen yada labarai na zamani, domin kokarin batar da ‘yan Najeriya, su karkatar da hankulan su daga matsalar da ta kunno kai ta ibtila’in cutar Korona da ta addabi duniya da ma kasar mu mai albarka, sannan a daya gefen kuma su bata sunan shugaba kuma jagoran Musulmin Najeriya baki daya, wato Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III. Wadannan bata-gari sun kirkiri wata karya, sun yada ta, domin kokarin cimma wata mummunar manufa. Amma da yake Allah ba ya zalunci, kuma bai yarda da zalunci ba, sai aka wayi gari ya tona asirin su, kuma ya bankado wannan makirci da sharri na su!

Sun kirkiro wata karya, wadda duk wani mutum mai kishin addinin sa na Musulunci ran sa zai baci da ita. Suka ce wai mai Alfarma Sarkin Musulmi yace ‘annobar cutar Korona karya ce, babu ta.’ Sannan wai suka ce yace, ‘shi yayi yawo, ya ziyarci dukkan wuraren da aka kebe domin kula da masu wannan annoba, amma shi bai ga wata annoba ba, kuma bai ga masu fama da wannan annoba ba, shi abinda kawai ya gani shine masu fama da cutar zazzabin malariya.’

Ya ku ‘yan uwa na jama’ar Najeriya, ku sani, wallahi wannan labarin kanzon kurege ne, labarin karya ne, kuma wani irin shiri ne na mazambata, magauta, shedanu, makirai, wadanda basu nufin Musulunci, arewa da Najeriya da ci gaban alkhari. Domin nayi imani da Allah, wallahi, babu yadda za’a yi Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya fadi wannan magana. Domin duk wanda yasan Mai Alfarma Sarkin Musulmi, zai san da cewa ya wuce yayi irin wannan magana ta ‘yan gareji, ‘yan tasha, kuma magana irin wannan mai kama da zancen teburin mai shayi!

Alhamdulillah, ai ma duniya ta shaida, in dai zamu yi wa kawunan mu adalci, irin yadda NSCIA da JNI duka suna karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi ne, suka fito suka yi Allah waddai da irin miyagun malaman nan masu kokarin batar da mabiyan su game da sha’anin cutar Annobar Korona. Jaridu da sauran kafafen yada labarai duk sun buga wannan matsaya, duk mai bukata zai iya nema. Kuma duniya ta shaida, irin yadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi bai yi kasa a gwiwa ba, yake fadi-tashi, ba dare ba rana, na ganin cewa Allah ya takaita wannan ibtila’i. Amma da yake shi mugu mugu ne, azzalumi azzalumi ne, har kullun ba ya ganin alkhairi, sai dai kokarin kirkirar sharri, da ma abunda sam ba’ayi ba yace anyi.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, a matsayin sa na cikakken Musulmi mai imani, mai hankali, mai ilimi da hangen nesa, ya kira dukkan al’ummar Musulmi da ma dukkan ‘yan Najeriya cewa, mutane suyi hankali, suyi taka-tsan-tsan, domin cutar annobar Korona gaskiya ce, ba karya ba ce, kuma ba ba’a ba ce, ba kuma tatsuniya ba ce. Sannan kuma yayi gamsashshen bayani na irin yadda wannan annoba ta samu wasu ‘yan kasa. Yayi kira ga ‘yan Najeriya cewa su bi duk wani mataki da hanyoyin kariya na rigakafi daga wannan annoba mai hadari, kamar yadda hukumomin lafiya da duk wasu masu ruwa da tsaki suke bayyanawa. Kuma yayi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda. Sannan yayi kira mai karfi da a koma ga Allah, a tuba zuwa ga re shi, ayi istighfari, sannan ayi addu’a, a roki Allah domin ya yaye muna wannan jarabawa. Har ma ya kan yawaita maimaita wani take cewa, “YI IYA KOKARINKA KA BAR WA ALLAH SAURA…”, wanda wannan duk wani mai hankali yasan cewa gaskiya ne.

Wannan ita ce matsayar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma duk kungiyoyin Musulmi da ma al’ummar Musulmi suna tare da shi akan wannan, sai fa ‘yan tsiraru da suka fandare a bisa jahilci da rashin sani, ko kuma bin son zuciyar su. Muna rokon Allah ya shirye su, amin.

Ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kare mu, ya kare kasar mu, yayi muna maganin wannan annoba, ya kare mutunci da alfarmar shugabannin mu, amin.

Nagode,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. 08038289761.

Share.

game da Author