RASUWAR KYARI: Ga masu karyata coronavirus, wannan ya zama darasi a gare su – Boss Mustapha

0

Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar coronavirus, Boss Mustapha ya bayyana cewa yanzu dai kowa ya gani, coronavirus ba karya bace kamar yadda wasu ke yadawa.

Boss cikin halin juyayin rashin marigayi Abba Kyari ya ce wannan rasuwa ya girgiza shi matuka. Ya kara da cewa ga masu cewa coronavirus ba gaskiya bace yanzu dukkan mu mun gani, mun rasa na kusa da mu. Mu sani wannan cuta ba wasa bace, da gaske ta ke.”

” Idan da muna ganin ana rasuwa a wasu kasashen, yanzu gata ta zo kusa damu. Idan za a ba da labarin wadanda suka rasu a dalilin coronavirus, Za a ambaci marigayi Abba Kyari. Saboda haka mu maida hankali matuka wajen bin dokokin likitoci. Mu rika wanke hannayen mu, mu rika amfani da sinadarin tsaftace hannu da kuma yin nesa-nesa da juna a koda yaushe.

Mustapha ya kara da cewa duk da coronavirus da afko mana daga waje ne, InshaAllahu ba zai yi tasiri a Najeriya ba domin shugaba Muhammadu Buhari ya na kokarin ganin gwamnati ta yi duk abinda za ta yi don kare mutane daga cutar.

Marigayi Abba Kyari mutumin kirki ne kuma mai kishin kasa Najeriya. Marigayi Abba Kyari ba ya wasa a aikin sa musamman wadanda ya shafi tabbatar da kudirorin shugaba Muhammadu Buhari. Marigayi Abba Kyari, bai shakkun taka koma waye idan har zai kawo wa aikin da Buhari ya saka a gaba cikas. Burin sa shine Buhari yayi nasara a bainda ya san a gaba na gyaran Najeriya.

Marigayi Abba kyari ya rasu ranar, juma’a a wani asibiti a Legas. An yi jana’izar sa ranar Asabar a Abuja wanda babban Malami, Isa Ali Pantami ya jagoranta.

Duk da ba a yarda an cika wannan makabarta ba, Babagana Monguno, Sama’ila Isah Funtua, Sam Nda-Isaiah da wasu kalilan daga fadar gwamnati sun halarci jana’izan.

Share.

game da Author