Mahukunta a kasar Saudi Arabiya sun bayyana cewa a dalilin ci gaba da yaduwar coronavirus da ake samu, an yanke hukuncin cewa bana za a yi rika sallar tarawiyyi da salloli a watan ramadan a gida ne.
Ma’aikatan Harami me kawai za su halarci tarawiyyi, banda mutanen gari.
Sannan kuma za rage yawan raka’o’in da za ayi zuwa 6 tare da Shafa’i da witr duka raka’o’i 10 kenan.
Bayan haka an soke yin Itikafi a Ramadan din bana.
Mahukunta sun ce hakan ya zama dole a dalilin annobar coronavirus.
AbdulAziz Bn Abdullah Al-Sheikh, ya zo a tarihi cewa cewa Annabin tsira SAW, ya yi wadannan salloli a gida. Kuma ma Tarawiyyi ba farilla bane, Sunna ce.
Sannan ya kara da cewa idan ya kama hatta sallar Idi za a yi shi a gidaje. Kowa zai yi sallar sa ba tare da kutuba ba a gida.
Sannan yayi bayanin yadda mutane za su fidda zakkar kona idan lokaci yayi.
Haka kuma babban sakataren kungiyar hadin kan musulunci,Dr Yousef Al-Otheimin, Yace daya daga cikin hukunce-hukuncen shari’a shine kare lafiya da rayukan mutane kafin komai, musamman a wannan lokaci da duk duniya ke yaki da sabuwar annoba da ba a santa ba.
Haka Shafin arabnews da Haramain suka ruwaito a shafin su.
A Najerya ma, wasu gwamnatocin jihohi sun sanar cewa ba za ayi tafsirin watan ramadan a masallatai, sannan babu sallar tarawiyyi a masallatai saboda dakile yaduwar annobar coronavirus.
Haka kuma babban malami, Sheikh Ahmad Gumi, shima ya sanar cewa zai yi tafsiri a gida ne inda za arika watsawa ta yanar gizo.
Allah ya kawo mana karshen wannan annoba ya karbi ibadun mu.