RAMADAN: Buhari ya hori musulmai su kiyaye kan su sannan da yin Ibada tukuru a wannan watan

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Mika sakon taya murna ga musulmai kan zagayowar watan Ramadan.

” Wannan shekara za a yi azumin watan Ramadan cikin annobar COVID-19, da hakan yasa Mutane ba zasu samu samar yin abubuwan da aka Saba ba a baya.

Shugaba Buhari ya gargadi Jama’a a da su yi hakuri da matsalar da aka shiga a duniya da ya sa kasashe suka dakatar da taron Jama’a wajen yin sallolin Taraweeh, Tahajjud, da kuma salloli a masallatai. Hakan ya zama dole saboda kaucewa yada cutar coronavirus.

Ya kuma ya gargadi mutane kada su yi amfani da wannan annoba suki yin Azumi.

Buhari ya ce addinin musulunci bai bar mu banza ba domin an sanar da musulmi abubuwan dake sa a ki daukar Azumi, kamar su tsananin rashin lafiya, matafiyi da sauran su.

A karshe ya hori Mutane da kowa ya dage da Addu’o’i a cikin wannan watan Mai alfarma, watan Ramadan.

Share.

game da Author