RABON KUDIN TALLAFI: An yi wa bayanan su karkatattar fahimta – Shugabannin Majalisa

0

Shugabannin Majalisar Dattawa da ta Tarayya sun maida wa Hadimar Shugaba Muhammadu Buhari a Harkokin Tallafi da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Maryam Uwais raddi, bayan ta soki bayanan su da suka soki tsarin rabon kudaden tallafi da Gwamnatin Tarayya ta yi a karkashin Ma’aikatar Bada Agaji da Jinkai.

Sanata Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila sun nuna rashin jin dadin yadda aka bi aka tsara sunayen wadanda suka amfana da naira bilyan biyar da Minista Sadiya Farouq ta ce ma’aikatar ta ta raba wa marasa galihu.

Bayan sun nuna tababa da shakkun yadda aka yi rabon kudaden, Hadimar Buhari, Maryam Uwais ta fito ta soki lamirin su, ta ce shakkun da suka nuna abin takaici ne da kuma hatsari ga Najeriya.

A kan haka, Shugabaannin Majalisa sun sake fitowa suka nuna cewa ba a fahimci bayanan da suka yi ba ne, shi ya sa har ita Uwais ta ke tayar da jijiyar wuya.

Na farko sun ce babu inda suka nuna cewa tsarin rabon kayan tallafin ya gaza ba. Sannan kuma sun ce dukkan tsokacin da suka yi, sun yi ne domin kawo gyara yadda shirin zai kara inganci sosai.

Shugabannin Majalisa sun ce a lokacin da suke tsokacin, duk ita Minista Sadiya ta na rubutawa kuma ta nuna za ta karbi gyaran da suka yi mata da hannu biyu.

A kan haka ne suka ce hayagagar da Maryam Uwais ta yi, inda ta nuna kamar ta na magana ne a matsayin ta na wata garkuwar talakawa, tamkar cin fuska ne ga shugabannin.

Yayin da suka ce su na maraba tare da yin aiki tare da kowace hukuma ko ma’aikata, a daya gefen kuma sun ce kumfar bakin wasu jami’an gwamnati ba zai kashe musu guyawu daga yin gyare-gyare a dukkan wararen da suke ganin akwai bukatar su yi tsokaci domin a gyara ba.

Kumfar Bakin Maryam Uwais A Kan Shugabannin Majalisa

Hadimar Shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa Shugabannin Majalisar Datttawa da na Tarayya dirar mikiya, inda ta caccake su cewa, zargin su na shakkun yadda aka yi rabon kudin talladin rage kuncin zaman gida a lokacin jimamin Coronavirus, ta ce zargin su da shakkun su na gaskiya ba ne, kuma akwai hatsari a cikin kalaman na su.

Uwais ta fitar da wannan sanarwa ne bayan Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin MJalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila sun Nina rashin gamsuwa da yadda aka yi rabon kudi da kayan agajin tallafi, wato NSIP.

Shugabannin Majalisar Dattawa da Tarayya ba su yarda da tsarin rabon kudaden agajin Coronavirus ba

Shugaban Majalsar Dattawa da na Majalsar Tarayya, sun nuna rashin gamsuwa da rashin amincewa da tsarin da Ministar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a ta bi wajen rabon makudan kudaden da ta ce ta rabas ga talakawa domin rage musu radadin kuncin zaman gida a lokacin zaman kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.

Sanata Ahmed Lawan na Majalisar Dattawa, ya nuna rashin amincewar sa a gaban Minista Sadiya Farouq, lokacin da suka gayyace ta domin ta yi musu karin haske daga kura-kuran da jama’a da dama a kasar nan ke zargin an tabka nara rashin adalci a lokacin raba kudaden.

Lawan ya yi kira a gaggauta kafa dokar da za yi daidai da tsarin rabon kaya da kudaden tallafi na sauran kasashen duniya da duniyar ta amince da shi.

Lawan ya fito karara ya shaida wa minista cewa ba a yi adalci a wajen rabon ba, domin a cewar sa, ba wadanda suka cancanta ko suka wajaba aka bai wa kudaden ba.

“Domin idan an ce ta intanet za a tantance talaka ko aka tantance talaka, to kenan ba talaka na hakika aka raba wa kudin ba.

“Tantirin talaka fa ba shi da sukunin intanet ko banki ajiyar kudi, ba shi da lantarki kuma ba shi ma da lambar makullin asusun banki, wato BVN.

Daga nan Lawan da Femi Gbajabiamila sun nemi sadiya ta sauya tsarin bayar da kudaden gaba daya.

Ana ci gaba da sukar Sadiya dangane da yadda ta ce ta raba naira bilyan biyar ga talakawa a cikin kwanaki biyu.

Wasu na ganin ko naira bilyan biyu ba a ma raba.

Shi ma Sanata Lawan ya tambayi tssrin da aka bi aka raba kudaden da kuma yankuna ko jihohin da aka raba kudaden, kai da ma sauran tamayoyi masu dora shakku a kan Minista Sadiya.

Idan ba a manta ba, ta sha ragargaza a shekarar da ta raba dabinon tallafi daga Saudiyya a lokacin azumi, sa’adda ta ke shugabancin Hukumar Raba Kayan Agaji.

Yadda Mu ka Raba Kudaden Agaji -Maryam Uwais

” Ba gaskiya ba ne da Shugabannin Majalisa suka ce shirin Bayar da Tallafi (NSIP) ya karbi ya lamushe naira tiriliyan 2 daga 2016 zuwa yanzu.

“Da farko Majalisar Tarayya ta amince a cikin kasafin kudi a ba raba naira tiriliyan 1.7. Amma daga 2016 zuwa Oktoba, 2020 lokacin da aka maida komai a karkashin Ma’aikatar Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, naira bilyan 619.1 kadai aka ba mu. Wato kashi 36% bisa 100% kadai na kudaden.”

Maryam ta kuma karyata ikirarin da shugabannin majalisa suka yi cewa ta tsarin BVN suke raba kudade.

Ta ce kudaden rage kuncin talauci da ake tura wa mabukata a asusun ajiyar banki, daga Ma’aikatar Tsare-tsare ta Jihohi suka samu alkaluman wadanda ake bai wa kudaden, ba ta tsarin BVN ba.

Ta ce tsari ne da ake bi tun daga kananan hukumomi ana tantance wadanda suka cancanta su amfana.

Ta ce sai an tantance a ina gida ya ke? Mutum nawa ne a ciki? Maza nawa ne kuma mata nawa ne?

Maryam ta ce karya Shugabannin Majalisa ke yi da suka ce majalisa ta kasa gane tsari, matakai da ainihin ilahiri da adadin wadanda ke amfana da kudaden a gaskiyance.

Ta kara da cewa ana aika wa majalisa da kwafe-kwafen bayanan da ke tattare da duk bayanan da ake bukata na rabon kudaden.

“Da suka ce tsarin biyan kudaden tallafi ta rajistar NSR damfara ce, wannan abin takaici ne matuka, kuma ganganci ne, kasassaba ce kuma wauta ce.”

Maryam ya ce wannan shakku da tababa da Majalisa ta nuna zai iya zama barazana ga sake karbar kudaden da iyalan Abacha suka kimshe. Saboda shirin NSIP yarjejeniya ce da Bankin Duniya, masu sa ido a kan kudaden.

A karshe ta ce tun cikin Sarumba 2019 aka maida shirin a Karkashin Ma’aikatar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwa. Amma ta zabi ta maida martanin ne domin
da tukura da bako, duk Umbutawa ne, kuma abin da ya ci garin Doma, ba zai bar garin Awai ba.

Share.

game da Author