Dan gwamnan jihar Kaduna Bello El-Rufai ya roki ‘yan Najeriya mata da maza, yara da manya, game da irin kalaman da ya rika fesawa a yanar gizo a farkon wannan mako.
Bello El-Rufai ya bayyana cewa lallai yayi azarbabin gaske kuma ya tafka kuskure domin ba halin sa bane kuma ba irin koyarwar gidan su bane abin da yayi.
Yace lallai ya wuce gona da iri a lokacin da yake amsa mutumin da ya cakale sa inda ya hada har da kabilar sa sannan ya shiga gonar yaba kalaman cin zarafin iyaye a lokacin da yake amsa mutumin.
“ Bayan haka kuma na roki yafiya a wurin mahaifiyata da nasa cikin rudani duk a dalilin wadannan kalamai nawa. Da duka mata gaba daya.
Idan ba a manta ba Shafin tiwita ta dau zafin gaske tun daga ranar Lahadi zuwa ranar Litini, akan martani da Bello El-Rufai ya maida wa wani da ya tsakale shi yayi masa lakabi da ‘shagwababben dan Baba’
Wannan mai rubutu ya amsa wani rubutu ne da Bello yayi da ya ce gwamnatin shugaban Amurka ta gaza matuka a wannan lokaci da ake gwagwarmaya da cutar coronavirus a fadin duniya.
Wannan mai rubutu yayi wuf ya maida wa Bello martani da kalaman da ya tunzura shi, inda shima Bello ya aika masa da martani cewa ya iya wa bakin sa, idan ba haka ba ” Ka gaya wa mahaifiyar ka zan jefa ta ga abokai na da dare. Ba mu dai son a yi kuwa da yaren Ibo.”
Wannan Kalami ya sa wasu na ganin bai dace ta fito daga bakin Bello El-Rufai ba, wanda dan gwamnan jihar Kaduna ne, Nasir El-Rufai.
Wasu sun kushe wadannan kalamai, wasu kuma sun ce shi wannan mai karatu da ya fara tsakalar Bello shine silar koma me aka ce akan sa.
Wasu manyan kasar nan kamar tsohuwar ministan Ilmi, da ta yi aiki tare da mahaifin sa Oby Ezekwesili a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo ta nuna bacin ranta game da abin da Bello ya rika fadi tun bayan wannan rubutu da wannan mutumi yayi.
Sai dai Bello ya ce ba zai mai da takobin ba. Ya ce lallai zai ci gaba da maida wa koma waye martani idan ya tsakale shi ko kuma ya nemi ya ci mutuncin mahaifin sa, gwamna Nasir El-Rufai.
Shafin tiwita ta dau zafi matuka, inda wasu ke ganin lallai tsakalar Bello da wannan marubuci yayi shine silar tada wannan husuma. Da bai yi masa habaici da gorin cewa shi ‘shagwababben dan baba bane, da Bello bai fusata ya maida masa da martani da irin kalaman da yayi ba.
Wasu kuma na ganin duk da ya fadi masa wannan kalamai, bai kamata Bello ya harzuka haka ba ya saka iyaye a cikin raddin da ya maida wa wannan marubuci ba.
A karshe dai, Bello yayi barazanar maka dan jarida Samuel Ogundipe a kotu saboda yin labari akan abinda ya faru a tiwita cewa bai yi masa adalci ba yadda ya ruwaito labarin.
A bisani bayan tauna maganganun da danta yayi, uwargidan gwamna El-Rufai, Hadiza El-Rufai, ta fito ta soki wadannan kalamai na danta Bello, inda tace lallai yayi kuskure kuma zata yi masa fada akai.
Sannan kuma ta roki mata da ‘yan Najeriya da su yi hakurin rashin ganin kuskuren danta daga farko cewa bata karanta abinda kyau bane.
Discussion about this post