Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa dimbin ‘yan Najeriya d su k rika aiki masa d sakonnin wasikun ta’aziyya gare shi da kuma iyalan marigayi Abba Kyari, tsohon Shugaban Ma’aikatakan Fadar Shugaban Kasa.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar godiyar Buhari a ranar Litinin, inda ya ce ya gode wa yadda aka rika aiko da wasiku, ba tare da an rika yin tururuwa ana kai ziyarar ta’aziyya ba.
Ya ce ya ji dadin yadda masu ta’aziyya su ka kiyaye da ka’idojin da Hukumar NCDC ta bayar, inda ta umarci a daina haduwa da juna, kowa ya rika yin nesa da juna. Wannan inji shi ya sa an rik yi wa mamacin addu’o’i a gida.
Garba Shehu ya lissafa wadanda suka aika da sakonnin ta’aziyya ko suka Buhari tarho suka yi ta’aziyya, sun hada da: Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Sahel, Ibrahim Abani, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Essan, Sarkin Bauchi, Mansur Dan Ali, Bolaji Akinyemi da sauran su
Abba Kyari ya dazu a ranar 17 Ga Afrilu, bayan ya yi fama da cutar Coronavirus.
Ya rasu a wani asibiti da ke Legas.
Jakadun kasashe da dama da manyan ‘yan kasuwa duk sun aika wa Buhari da ta’aziyya. Jaka ma jakadan Najeriya da ke wasu kasashen da ‘yan kasuwa da sauran manyan malamai.