Kungiyar Kare Hakkin musulmai karkashin shugabancin Ishaq Akintola, ta bayyana cewa akwai makarkashiyar da ake yi na rage yawan musulmai a Najeriya, ganin yadda aka bari mutane ke ta mutuwa a Kano da kuma rashin wuraren gwajin Coronvirus da ba a dasu a garin Kano din.
” Abin tashin hankali shine yadda hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDC suka ki kakkafa wuraren gwaji a jihar sannan kuma idan aka kira su game da coronavirus ba su amsawa.
” Cibiyar da ake gwajin cutar dake asibitin Aminu Kano, ita an kulle ta, saboda haka a ina ne hukumar NCDC ta samu yawan mutanen da suka ce sun kamu da cutar a Kano.
” Muna kira da a gudanar da bincike game da rashin kakkafa wuarren yin gwajin cutar a Jihar da yankin Arewa, domin nan ne Musulmai suke da yawa, kuma kada a kuskura a shirya makircin da zai rage yawan musulmai a kasar nan.
Bayan haka ya yi kira ga mutanen Jihar Kano da Najeriya, da su bi uamrni da dokokin mahukunta, su rika wanke hannaye, zaman gida da kuma yin Nesa-nesa da juna.
Sai dai kuma wannan zargi da Akintola yayi ya sha suka domin wasu da dama harda musulmai sun karyata zance sa. Wasu na zargin sa da nema tada zaune tsaye da nuna bambamcin addini a kasar nan.