Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku na Kasa, Jafaru Ahmed, ya bayyana ce kashi 70% bisa 100% na wadanda ke tsare a gidajen kurkukun kasar nan, duk wadanda ba a kai ga yanke musu hukunci ba ne.
Da ya ke magana a ranar Alhamis, yayin kwarya-kwaryan bikin sallamar wasu daurarru da aka yi wa afuwa a Abuja, Ahmed ya ce akwai daurarru a gidajen kurkuku daban-daban a fadin kasar nan har 73, 726.
Ya ce amma 51, 983 duk jiran a yanke hukunci su ke yi.
Wannan bayani ya kara fito da wani zargin da ake yi a kasar nan cewa, yawancin wadanda ke tsare a kurkuku daban-daban na kasar nan duk ba da laifin su ake tsare da su ba.
Wata kudiddiga da Hukumar Kididdigan Al’kaluma ta Kasa (NBS) ta gudanar a baya ta nuna tsakanin 2011 zuwa 2015 akwai kashi 72.3% na daurarrun kasar nan duo ‘yan zaman jiran a yanke musu hukunci ne.
Bincike ya nuna da yawa ana jibge su a kurkuku a manta da su, wasu kuwa a shafe shekaru masu yawa ana doguwar shari’a.
Akwai kuma wasu da dama sa jami’an tsaro kan damke ba da laifin su ba, a karshe a je a jibge su a kurkuku su shafe shekaru da dama ba tare da yanke hukunci ba.
An dai sallami daurarru 70 a kurkukun Kuje da ke Abuja, inda a wurin sallamar ta su Shugaban Kula da Gidajen Kurkuku ba Kasa ya ce daurarru sun yi yawa sosai a kurkuku, har ma sun cunkushe.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin rukunonin daurarru biyar da wannan aduwar ta shafa, inda Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi wasu daurarru 2600, domin kauce wa cunkoson kamuwa da cutar Coronavirus a kasar nan.
Da ya ke jawabi a Hedikwarar Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa, Aregbesola ya ce wanan afuwa da aka yi musu ta na bisa tsarin rage yawan cinkoso a gidajen kurkuku ne da aka ce za a yi, ganin yadda cutar Coronavirus ta bulla gadan-gadan a Najeriya.
Ga Wadanda Za A Yi Wa Afuwa Nan
Jaridar Punch ta ruwaito Aregbesola na cewa rukunin daurarrun da za a yi wa afuwa, sun hada:
1. Daurarrun da suka shekara 60 a duniya abin da ya yi sama.
2. Daurarru marasa lafiya, kuma a bisa dukkan alamu rashin lafiyar ta su a iya cewa ciwon ajali ne.
3. Wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekara uku abin da ya yi sama, sannan kuma bai fi watanni shida su kammala wa’adin daurin na su a kurkuku ba.
4. Daurarrun da ciwon tabin hankali ya same su.
5. Daurarrun da aka yanke wa zabin biyan diyyar da ba ta wuce naira 50,000 ba, amma suka kasa biya.
Wadanda Ba Za A Yi Wa Afuwa Ba
Minista ya ce su ne rukunin daurarrun da aka kama da manyan laifuka irin su ta’adda ci, fashi da makami, gsrkuwa da mutane, kisa da kuma fyade.
Ya kara da cewa za a saki fursunonin farko daga kurkukun Kuje da ke Abuja. Daga nan kuma za a tsara yadda yadda za a ci gaba da sakin sauran a kurkukun fadin kasar nan.
Shi ma Ministan Shari’a Malami, ya ce zai ci gaba da yin afuwar kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta shawarci kowace kasa ta rage yawan daurarru domin a rage cunkoso a gidajen kurkuku, ganin yadda annobar Coronavirus ta barke a duniya.