Wata kungiya mai suna Kungiyar Sa-ido Kan Yadda Ake Kashe Kudaden Da Aka Dawo Da Su Bayan An Sace Daga Najeriya (MANTRA), sun bayyana cewa su na shaida Gwamnatin Tarayya ta kashe naira bilyan 23.7 daga naira bilyan 125 da aka dawo da su, na kudaden da aka sace a lokacin mulkin tsohon Shugaban Mulkin Soja, Sani Abacha.
Kungiyar MANTRA ta ce ta gamsu am an raba wa talakawa da sauran marasa galihu kudaden ta hanyar Shirin Tallafa Wa Masara Galihu Kudade Cikin Kai-tsaye Cikin Asusun Bankin Su.
Rahoton da kungiyar ta fitar ta ce an raba wadannan zunzurutun makudan kudade bisa umarnin da Shugaban Kasa ya yi cewa a tallafa wa marasa galihu, saboda su dan ji saukin radadin zaman gida, saboda Coronavirus.
Wata kungiya mai suna ANEEJ, wadda da rahoton ta ne MANTRA ke tinkahon kafa hujja, ta ce an biya masara galihu kudaden ariyas tun daga na watan Janairu zuwa Afrilu da wadannan kudade naira bilyan 23.7.
ANEEJ ta ce ta jagoranci gamayyar wasu kungiyoyin sa-ido, wadanda suka yi aikin duba-garin yadda aka yi rabon kudin.
Gudun Kada Sata Ta Saci Sata
Cikin 2017 ne Gwamnatin Switzerland ta maido wa Najeriya dala milyan 332.5, kwatankwacin naira bilyan 125, daga cikin makudan kudaden da Sani Abacha ya sace daga Najeriya ya boye a can kasar.
Sai dai kuma an kafa yarjejeniya cewa Bankin Duniya (World Bank) tare da wasu kungiyoyi za su sa ido a kan yadda talakawa za su amfana da kudin, don gudun kada wasu batagarin jami’an gwamnati su sake sace kudaden.
David Ugorlo, wanda shi ne Shugaban Kungiyar ANEEJ, ya ce MANTRA ta bi diddigin yadda aka bai wa marasa galihu har mutum 73,998 a cikin kauyuka sama da 4,500 cikin kananan hukumomi 97, kuma sun shaida duk sun karbi tallafin kudaden a cikin jihohi 20.
Daga nan ya kara yin bayanin wasu matakan da suka kara bi wajen tantancewa.
Ya koma lissafo wasu kungiyoyi da ya ce an yi aikin sa-idon tare da su, da suka hada da: CSJ, CHRISED, BANGOF, FAHIMTA, FAWOYDI, NISD da sauran su.