Ministar Harkokin Agaji, Tallafi da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa kafin su raba shinkafar agaji da tallafi, sai da Hukumar Kiyaye Lafiyar Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta fara dandanawa da auna lafiyar shinkafar.
Sai dai kuma NAFDAC ta ce kwata-kwata ba a gayyaci jami’an hukumar ba domin duba shinkafar kafin a raba ba.
Musamman NAFDAC ta ce ba ta ma san an raba shinkafar jihar Oyo, wadda ake tankiya kan gurbacewar ta ba.
Gwamnatin Tarayya ce dai ta bada umarnin a raba wa jihohin Oyo, Osun da Ekiti kowace buhunan shinkafa 1,800 jihar Ondo kuma buhuna 8,00, a matsayin abincin tallafin rage radadin kuncin rayuwa lokacin Coronavirus.
Sai dai kuwa kwanaki uku bayan raba wa Oyo buhuna 1,800, Hadimin Gwamna mai suna Debo Akande ya kira taron ‘yan jarida, inda ya shaida musu cewa, “buhunan shinkafa 1,800 da aka bai wa jihar Oyo duk rubabbiyar shinkafa ce, bai dace mutane su ci ta ba.
Shinkafar da daga hannun Hukumar Kwastan ta Kasa aka karbe ta aka raba wa jihohin.
Sai dai kuma a na ta martanin, Ministar Tallafi da Agaji Sadiya Farouq ta ce, ” mun karbi shinkafar daga hannun Hukumar Kwastan ta Kasa.
“Sannan kuma kafin mu raba ta, sai da mu ka gayyaci Hukumar NAFDAC ta auna shinkafar, ta tabbatar da lafiyar ta, sannan ta ba mu takardar amincewa a raba wa jama’a shinkafar.”
Sai dai kuma Hukumar Kwastam Reshen Oyo da Osun ta ce jihar Oyo ba ta yi wa Kwastan adalci ba.
Kakakin Kwastan na yankin, Abdullahi Lagos, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa su na zargin Gwamnatin Oyo da yin rufa-rufa a lamarin.
“Mun bai wa Oyo buhuna 1,800, haka ma Osun da Ekiti. Ondo kuma buhuna 800. Kuma dukkan su ba mu ne mu ka zabar musu ba. To me ya sa Oyo ce kadai za ta ce an ba ta gurbatacciyar shinkafa?”
Sai dai kuma Shugabar NAFDAC Mojisola Adeyeye, ta ce an dai gayyaci jami’an hukumar ta zuwa Idi-Iroko, Akija da Ogun domin su debi samfurin shinkafar kuma su gani da idon su. Amma ba a ce su je su auna ta har su bayar da satifiket din ingancin ta ba.
Haka dai Adeyeyi ta furta a hirar da aka yi da ita a gidan talbijin na Channels.
Ta ce sannan babu wanda ya kira NAFDAC domin su duba shinkafar da aka raba wa jihar Oyo.
Ita kuwa Sadiya ta hakikice cewa “NAFDAC ta Cuba shinkafar kuma ta bayar da satifiket, wanda ta ce za ta fito da shi a ranar ta nuna wa duniya.
“Ina ganin an dan samu rashin tuntubar bayanai ne tsakanin Kwastan da NAFDAC. Amma dai za a warware wannan rashin tuntubar a tsakanin su.” Inji Minista Sadiya.