Marigayi Abba Kyari, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Muhammadu Buhari, ya rasu narar 17 Ga Afrilu. Kuma shi ne mutum na 17 da cutar Coronavirus ta kashe a Najeriya.
Tsohon dan jarida ne, wanda har mukamin Mataimakin Edita na jaridar The Democrat ya rike a Kaduna, a lokacin da Abdulkarim Al-Bashir ke Editan jaridar.
Tsohon ma’aikacin banki ne da ya rike mukamai daban-daban, har da shugabancin First Bank.
Ya rasu bayan ya kamu da cutar Coronavirus, tsawon kwanaki 25 ya na jiyya. Ya kamu da cutar, ko kuma a ce an tabbatar da cutar a jikin sa, a ranar 23 Ga Maris, 2020.
Tun daga lokacin ne ya yi sanarwar killace kan sa.
Amma a ranar 29 Ga Maris, marigayi Kyari ya yi sanarwa mai ratsa jiki a shafin sa na Twitter, inda ya yi bayani a takaice kamar haka:
“Ina sanar da ku cewa zan bi shawarar da aka ba ni, wato za a maida ni wani asibiti a Lagos domin ci gaba da kula da lafiya ta a yau.
“Duk da dai ni dai har yanzu lafiya kalau na ke jin jiki na, amma gwaji ya tabbatar da cewa ina dauke da cutar Coronavirus, mummunar cutar da ke ci gaba da share rayukan jama’a a duniya.
“Ina sa ran dawowa a kan mukami na, na ci gaba da kasancewa a ofis, tare da zakakuran ma’aikatan da ke karkashi na, masu jini a jika. Za mu ci gaba da yi wa Shugaba Buhari aiki kamar yadda mu ka rika jajircewa mu na yi….”
Allah Sarki! Abba Kyari bai koma ofis din sa ko kan mukamin sa ba. Amma dai an koma da gawar sa Abuja, inda aka binne shi a can.
A Najeriya shi ne na 17 da cutar ta kashe. A duniya kuma shi ne cikon na 154,311 da suka mutu sanadiyyar Coronavirus, idan aka yi la’akari da kididdigar karfe 7 na safen ranar 18 Ga Afrilu.
Duk da dai Kyari bai bayyana yadda aka yi ya kamu da cutar Coronavirus ba, amma sahihan bayanai da majiyoyi sun tabbatar da cewa ya kamu da cutar a ziyarar aiki da suka kai kasar Jamus, shi da Ministan Makamashi, Saleh Mamman.
Sun kai ziyarar ce a ranar 7 Ga Maris zuwa 14 Ga Maris, inda suka tattauna batun aikin hasken lantarki na Mambilla, tare da kamfanin Siemens AG, bisa gayyatar Shugabar Jamus, Angela Mikel.
Babban abin da jama’a za su fi jiran gani a yanzu shi ne wanda zai maye gurbin sa.
Discussion about this post