Majalisar Kolin Musulunci ta bayyana yadda za’a rika bizne gawar masu cutar Coronavirus

0

Majalisar Kolin Musulunci ta bayyana cewa ya zama tilas a rika kauce wa yadda za a illata jama’ar da ke raye, a lokacin bizne gawar wanda cutar Coronavirus ta kashe.

Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin wasu ka’idoji da sharudda da Majalisar ta NSCIA ta gindaya domin yadda za a rika sallata da kuma bizne gawarwakin masu cutar Coronavirus.

Hakan ba zai rasa nasaba da yadda aka samun rudanin kauce ka’ida da kuma gwamutsuwar da aka yi ba a lokacin rufe gawar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, a Abuja.

Sani Gwarzo da Yusuf Onoha ne suka sa wa sanarwar hannu, a matsayin su na karamin kwamitin da aka nada, kuma aka dora masa nauyin yadda zai fitar da ka’idojin sallar gawa d bizne ta idan cutar Coronavirus ce ta kashe ta.

Daga cikin matsayar da suka cimma, sun ki yarda a rika kone gawar musulmin da cutar Coronavirus ta kashe, kamar yadda addinin Musulunci ya yi hani da kone gawar musulmi.

Sannan kuma domin gudun kada cutar da ke jikin gawar ta shafi masu wankan ta ko masu hidimar bizne ta, sun amince cewa sai jami’an lafiya ne kadai za su rika taba gawar.

Su kan su jami’an lafiya din sai dai su rika yayyafa wa gawar ruwa, domin kada su rika dakuna gawar har su kamu da cuta.

Sun kuma umarci a nunke mamaci namiji da likkafani nunki uku, ita kuma mace mai nunki biyar.

Ba su amince a rika yi wa gawar musulmi rufewar burbudewa a cikin rami ba tare da wasu gawawwakin da ba na musulmai ba.

Sun nemi lallai a rika rufe gawar musulmi a makabartun musulmai kawai.

Daga nan sun nemi ya kasance gwamnati za ta rika daukar dawainiyar bizne gawar, gudun kada a damka shi ga wasu mutanen da ka iya kamuwa da cutar.

Sannan kuma kada a bar masu cutar asma, tarin TB ko HIV su kusance shi, saboda za su fi kowa saurin daukar cutar.

Share.

game da Author