Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi tir da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a yankin Kananan Hukumomi Uku na jihar Katsina inda akalla mutane 47 suka rasa rayukan su.
Akalla mutum 47 ne mahara suka kashe a harin da suka kai kananan hukumomin Dutsinma, Danmusa da Safana, jihar Katsina.
Kakakin ‘yan sandan jihar Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ce tuni an aika da jami’an tsaro yankunan domin samar da zaman lafiya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a takarda da kakakin fasar shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, yanar Lahadi ya na mai cewa hakan ya yi matukar tada masa hankali da bacin rai sannan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya a dalikin aukuwar irin wannan abu cewa gwamnati za ta ci gaba da maida hanksli wajen fatattakar ire-iren wadannan miyagu da tarwatsa duk wani shiri na su na makirci.
Ya kara da cewa a wannan lokaci da mutane ke kokain kare kan su daga cudanya da juna, da zama a gida miyagu kuma na afka musu, hakan ba zai samu gindin zama a wannan gwamnati ba.
Shugaba Buhari yace ba zai lamunci
yawaitar kashe-kashen mutane haka kawai daga wasu ‘yan tadda ba, sannan ya ce lallai za a maida wa wadanda suka aikata wannan mummunar abu martani, cewa za su gamu da fushin jami’an tsaron kasa.”
Shugaba Buhari ya umarci Jami’an tsaro
da su kara kaimi wajen aikin samar da tsaro ga ‘yan Najeriya, sannan kuma su toshe duk wata kafa da ke ba wadannan ‘yan ta’adda damar afkawa mutane.
Sannan kuma ya jajanta wa iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukan su a wannan hari.
A karshe kuma ya hori mutane da su rika sanar da jami’an tsaro bayanai da ayyukan wadannan muggan mutane domin abi su a kakkabe su.