Idan ba a manta ba Mahara dauke da manyan bindigogi sun yi garkuwa babban wan gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, Adamu Mohammed.
Rahotanni a lokacin sun nuna cewa maharan sun diran wa gidan Adamu Mohammed da aka fi sani da Yaya Adamu a wannan rana ne.
Adamu Mohammed sananne ne a garin Bauchi kuma gashi dan uwan gwamnan jihar Bala.
Maharan da suka afka gidan Adamu, sun bude wuta tun daga kofar shiga gidan ne har suka waske da shi.
A ranar Talata maharan suka sako yaya Adamu,daga nan sai ya garzaya ya gana da ‘yan uwa da abokan arziki.