‘Yan bindiga sun far wa Kauyen Kaikai ranar talata inda suka kashe tsohon shugaban karamar hukumar Ganye, Sabastine Samsu Kaikai.
Wani da abin ya faru a idon sa ya bayyana cewa maharan sun diro wannan kauye ne da dare suka rika bude wuta ta ko ina.
Jin haka ke da wuya, Sai kakai da yake kauyen domin bukin Easter, ya ne ne ya arce daga gidan sa.
” Daga nan ne fa suka harbe shi nan take ya mutu.
Hukumumi sun tabbatar da aukuwar wannan abin tashin hankali.
Discussion about this post