Mahara sun kashe mutum 8, sun saka dokar hana walwala a kauyukan jihar Neja

0

Akalla mutum 8 ne wasu mahara suka kashe a kauyen Madakar dake karamar hukumar Rafi a jihar Neja.

Shugaban ‘yan bangan kauyen Madakar Isiya Madakar ya shaida haka wa PREMIUM TIMES.

Isiya ya ce maharan sun far wa kauyen dauke da manyan bindigogi da jigidar harsasai, harda bama-bamai.

Ya ce ‘yan bangan Madakar da ‘yan bangan dake kauyukan dake kusa dasu suka tunkari maharan.

” An kashe mana mutane 8 har da shugaban ‘yan bangan kauyen Mariga. Amma kuma mun kashe maharan da dama domin basu ji dadi ba.

Bayan haka kwamishinan ‘yan sanda Usman Adamu ya tabbatar da aukuwar haka inda ya ce rikici ne tsakanin barayin shannu da ‘yan banga.

Adamu ya ce bashi da masaniya ko a dalilin harin mazaunan karamar hukumar sun yi hijira daga gidajen su.

A ranar Talata ne rundunar sojin Najeriya ta sanar a shafinta na twitter cewa rundunar ‘Operation Gama Aiki’ ta fatataki keyan wasu mahara dake kauyen Maguga a karamar hukumar Rafi.

Hare-Haren ‘yan bindiga

Wani matashi kuma mazaunin karamar hukumar Rafi Abdulateef Lawal ya ce babu abin da rundunar sojin Najariya take yi domin maharan suna abinda suka ga dama a wannan yaki.

“A makon da ya gabata mahara sun far wa kauyen karamar hukumar Rafi inda mazaunan garin suka yi hijira zuwa wasu kauyuka mafi kusa da su wasu kuwa suka tare a sansanin ‘yan gudun hijira dake makarantar firamaren Bosso.

Daga nan kuma shugaban Kungiyar matasan kauyen Madaka Yusha’u Ibrahim ya ce watanni biyu da suka gabata mahara sun kafa dokar hana walwala a kauyen daga karfe 7:00 na dare zuwa 4:00 na safe.

Ibrahim ya kuma ce tsakanin tsakiyar watan Maris zuwa tsakiyar watan Afrilu mahara sun buwayi mutanen kauyen da hare-hare inda a dalilin haka suka yi garkuwa da mutum 21 sannan suka kashe mutum biyar a kauyen.

Ibrahim ya yi kira ga gwamnati da ta aiko da Jami’an tsaro zuwa karamar hukumar su domin samar miusu da tsaro.

Share.

game da Author