Mahara sun kashe mutane 9, sun babbake gidaje 33 a jihar Filato

0

A cikin wannan yanayi da mutanen kasa ke fama da ci gaba da yaduwar annobar coronavirus, mahara basu kyale mutane sun zauna lafiya ba a Najeriya.

A jihohin Filato da Taraba, ‘yan bindiga sun far wa mutane a gidajen su, kuma sun kashe mutane da dama a hare-haren da suke kai wa.

Akalla mutum 9 ne suka mutu a harin da wasu mahara suka kai a masarautar Irigwe dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Bayan haka, sun babbake gidaje 33 a wannan masarauta bayan kashe mutane da suka yi.

Shugaban Kungiyar raya masarautar Irigwe (IDA) Sunday Abdu ya Sanar da haka ranar Alhamis da ya ke zantawa da Kamfani Dillancin Labaran Najeriya yana mai cewa maharan sun far wa masarautar ne a daren Talata.

Abdu ya ce mutum biyu sun ji rauni a wannan harin kuma ana duba su a asibiti.

Ya ce a kwanakin baya ma wasu maharan su far wa masarautar inda suka kashe mutum 10.

Ya yi kira ga Jami’ar tsaro su gaggauta samar da tsaro a masarautar.

Shugaban yada labarai na rundunar ‘Operation Safe Haven (OPSH) dake jihar Filato Ibrahim Shittu ya tabbatar da haka inda ya ce kwamandan rundunar Chukwuemeka Okonkwo ya ziyarci masarautar ranar Laraba sannan ya ce za a samar da tsaro a wurin da sauran wuraren dake jihar Filato.

Idan ba a manta ba a ranar 14-ga watan Afrilu ne Boko Haram suka kai wa wasu tafiya hair a auno wanda ke kilomita 20 kafin Maiduguri, babban birnin jihar Barno.

Boko Haram sun kashe mata guda bakwai tare da banka wa mota mai dauke da buhunan wake wuta.

Share.

game da Author