Ma’aikatan kiwon lafiya 113 sun kamu da coronavirus a Najeriya – Minista Ehanire

0

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa ma’aikatan kiwon lafiya 113 ne suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

Ya fadi haka a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 ta yi a Abuja ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata Ehanire ya sanar cewa ma’aikatan kiwon lafiya 40 sun kamu da cutar a kasar nan.

Ya ce bayan mutum 40 din da suka kamu da cutar an killace wasu ma’aikatan na tsawon makonni biyu a dalilin kamuwa da cutar.

“Da dama daga cikin ma’aikatan da suka kamu da cutar na aiki a asibitoci masu zaman kansu ne sauran ma’aikatan asibitocin gwamnati.

“Domin gujewa irin haka ne gwamnati ta dage kan yin aiki da ma’aikatan kiwon lafiya da aka horas kan hanyoyi dakile yaduwar cutar.

“Hakan ya sa gwamnati ta hana asobitoci masu zaman kansu kwantar da mutanen da suka kamu da cutar saboda rashin samun horo na kwarewa.

Bayan haka Ehanire ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya dake kula da mutanen da suka kamu da coronavirus da su rika amfani da kayan samun kariya daga kamuwa da cutar a duk lokacin da za su duba wani mara lafiya domin gujewa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author