‘LOCKDOWN’: Masu karkatar da kayan tallafi tamkar cutar Coronavirus ce suke kinkima zuwa gidan su

0

Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Ramatu Aliyu, ta antaya tsinuwa ga duk wani jami’in Hukumar FCDA wanda ya karkatar da kayan tallafin Coronavirus zuwa gidan sa.

Da ta ke bayani wajen rabon kayan tallafi a Karamar Hukumar Kwali, ta bayyana cewa duk wanda ya karkatar da kayan tallafin Coronavirus zuwa gidan sa, ya sani cewa tamkar cutar Coronavirus ce ya kinkima zuwa gidan sa.

Daga nan sai ta yi kira ga jami’an rabon tallafin su yi aiki tsakani da Allah tare da yin rabo mai adalci.

“Wadannan kayan tallafin na kowa ne, babu wani bambancin yare ko addini. Duk wani jami’in rabon wadannan kayan ya sa ni shi ne wakilin mu a cikin jama’a. Kuma da abin da suka aikata ne za a auna kimar mu.”

Minista Ramatu ta ce wadannan kaya na al’umma marasa galihu ne. Don haka kada wanda ya jida zuwa gida.

“Ba kayan watanda ba ne. Idan watanda za ka yi, to ka je kasuwa ka sayo da kudin ka kawai.

“Ina hada ku da Allah, kada ku kwashe kayan tallafin nan. Wannan kayan abinci ba kayan kamfen din siyasa ba ne.” Inji ta.

A jihohi da dama dai jama’a na zargin cewa jami’an rabon kayan tallafi na karkatar da kayayyakin. Sannan kuma an ikirarin wasun su na zabtare kudaden tallafi da aka raba wa talakawa.

Wasu ma na zargin cewa mafi yawan kayan da ake cewa an raba, duk shaci-fadi da kintace ne kawai, amma ba a raba adadin ba.

Share.

game da Author