Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Barno Salihu Kwaya-Bura ya bayyana cewa likitoci 7 sun kamu da cutar Covid-19 a jihar.
Ya fadi haka ne ranar Juma’a a zaman da kwamitin dakile yaduwar cutar na jihar ta yi a garin Maiduguri.
Kwaya-Bura ya ce mutum 15 sun kamu da cutar a jihar sannan biyu sun mutu.
“Mun gano mutanen da suka yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar sannan mun killace su domin yi musu gwajin cutar.
Bayan haka Kwaya-Bura ya yaba wa bin dokar zaman gida dole da mutane suka yi a jihar.
Ya ce gwamnati za ta sassauta dokar domin ganin masu Santa’s abinci sun gudanar da aiyukkansu domin masu azumi su samu abun yin bude baku.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne Kungiyar likitocin jihar Legas ta bayyana cewa likitoci 3 sun kamu da cutar Korona Baros a jihar.
Kungiyar ta ce likitoci na aiki ne a asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas da asibitin Alimosho.
Likitoci na samun magani a asibitocin kula da mutanen da suka kamu da cutar a jihar.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun fara neman mutanen da suka yi cudanya da lokitocin domin killace su da yi musu gwajin cutar.
Kungiyar ta yi kira ga duk ma’aikatan kiwon lafiya da su guji duba mara lafiya ba tare da sun saka kayan samun kariya daga kamuwa da cutar.
Kungiyar su za ta tattauna da gwamnati domin tsara hanyoyi kare ma’aikatan kiwon lafiya da biyansu alawus domin karfafa gwiwowinsu a lokacin da suke aikin kula da masu fama da cutar a kasar nan.