Kungiyar ‘Yan Jarida sun meni wadanda suka halarci jana’izar Abba Kyari su daina zuwa taron ganawa da su

0

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa, Reshen Babban Birnin Tarayya, sun bayyana kyamar dukkan Mambobin Kwamitin Wayar Da Kai Kan Cutar Coronavirus, wadanda su ka halarci jana’iza da kuma binne gawar marigayi tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.

‘Yan jaridar sun ce daga yau ba su bukatar duk wani wanda ya halarci binne gawar ya sake halartar taron manema labarai da ake yi da su.

Shugaban Kungiyar, Emmanuel Ogbeche, ya roki mambobin na PTF, ciki kuwa har da Shugaban Kwamitin, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, cewa su rufa dimbin jama’a asiri, su janye jikin su, domin kada su goga wa ‘yan jarida da sauran wadanda ba su halarci binne gawar ba, wani alakakai din da duk su ka jangwalo a wurin.

“Mu ma mun bi irin sharuddan da Fadar Shugaban Kasa ta gindaya wa Mambobin Kwamitin Yaki da Coronavirus, cewa duk wanda ya halarci jana’iza a Defense House da wadanda su ka je Makabartar Gudu wurin bizne gawar Abba Kyari, to ya killace kan sa tsawon kwanaki 14, kafin ya sake shiga jama’a.”

Ogbeche ya yi kira ga ‘yan jarida cewa da zarar sun ga wani mamba a wurin taron ganawa da manema labarai, wanda suka tabbatar ya halarci bizne gawa ko ko jana’iza, to su gaggauta ficewa daga dakin taron, gudun kada su jefa rayuwar su a cikin hadari.

A karshe ya yi kira ga kafafen yada labarai su rika biyan wakilan su da ke daukar labaran bayanan Coronavirus kudaden alawus na saida-rai, wanda suke yi a kowace rana.

Kasar nan baki daya ta cika da mamakin ganin yadda dandazon manyan jami’an gwamnatin Buhari suka gwamutsu wurin bizne gawar Abba Kyari, duk kuwa da cewa wadanda suka halarci makabartar, su ne ma manyan jami’an yaki da cutar a kasar nan.

Sannan kuma kafofin yada labarai sun yi mamakin yadda aka yi taron bizne gawar Kyari, sun kuwa da cewa kwanan baya Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya ce gwamnati ba za ta rika bayar da gawar duk wani mamacin da Coronavirus ta kashe a hannun iyalan sa ba.

Share.

game da Author