Kotu a Legas ta umarci tsohon Mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar da Darektan Kamfen din sa a zaben 2019, Bukola Saraki, su biyata diyyar naira Miliyan Biyar saboda amfani da hotonta ba tare da izinin ta ba a lokacin Kamfen.
Matar maisuna Amudat Adeleke ta ce Atiku da Saraki sun dauke su hotuna a lokacin da suka zo kamfen Legas, kwatsam bayan dan wani lokaci sai ta rika ganin hotunan a wurare dabam-dabam manya-manya a na kamfen da su.
Tace Atiku, jam’iyyar sa ta PDP basu shawarce ta a lokacin da suka buga wannan hoto suka yada.
Ta roki kotu ta tilasta su biyata naira Miliyan 45 kudin diyyar saka hotunanta da suka yi ba tare da izinin ta ba.
Sannan kuma tace wannan hotu kamar yadda ya nuna, ta yi kamar it matsiyaciya ce, miskiniya wadda ke neman taimako ruwaa a jallo, wadda ba haka bane.
Akarshe Alkalin kotun ya umarci Atiku da Saraki su biyata naira miliyan 5 kudin diyya.