Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, ya bayyana cewa ya zama dole a tashi a magance matsalar almajirai a kasar nan, idan ba haka ba kuwa, nan gaba a wayi gari su zame wa jama’a da gwamnati babban alakakai.
“Babu wani abin damuwa don yara kanana sun tashi su na neman ilmin abin da zuciyar su ta yi imani da shi.
“Amma dai akwai bukatar a samar musu sana’o’in hannu da kayan aiki. Kuma a koya musu sana’o’in. A ba su ilmi a cikin jihohin su, ta yadda za a ci moriyar su a cikin al’umma nan gaba.
“Idan ba haka ba kuwa, to mu na kyankyashe wa kan mu wasu dakarun da za a wayi gari nan gaba su addabe mu, kuma su addabi kasar nan har mu rasa yadda za mu yi da su.”
Mustapha ya na magana ne dangane da aniyar Gwamnonin Arewa ta fara kamen almajirai da suka fara yi, su na maida su jihohin su na asali.
An kiyasta cewa akwai yara sama da milyan 10 a Arewa masu watangaririya kan titi ba su zuwa makaranta, kuma mafi yawan su duk almajirai ne.
Kwanan nan Jihar Kano ta bayyana cewa ta kwashi almajirai 1098, wadanda ta maida jihohin su.
Ta tura 419 a Katsina, 524 a Jigawa sai wasu 155 a Kaduna.
Rahotanni daga Kaduna sun ce biyar da Kano ta maida wa jihar Kaduna su na dauke da cutar Coronavirus.