Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ta ce kashi 25 bisa 100 ne kadai na ‘yan Najeriya za su amfana da tallafin kudade da abincin rage radadin kunci da za a raba kwanan nan.
Da ta ke tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, Sadiya ta ce a wannan karon za a damka rabon abincin ne ga gwamnatocin jihohi, domin gudun kada a sake samun cikas din da aka samu a rabon da aka yi na baya.
“Za a raba abincin da kudaden ko’ina, amma dai a kowace jiha ko gari, to kashi 25 bisa 100 ne kadai za su amfana da tallafin kudaden da na abincin.
Ana dai ci gaba da ragargaza da kuma neman sanin yadda aka raba kudaden tiryan-tiryan ga wadanda aka yi ikirarin cewa an raba musu.
Shugabannin Majalisar Tarayya da na Dattawa su ma ba su gamsu da yadda aka yi rabon bilyoyin kudaden farko ba.
Talakawan Cikin Birnin Kadai Za A Raba Wa Kudin -Sadiya
Minista ta kara da yin bayanin cewa za a raba kudaden da kayan abincin ne ga talakawa da fakirai da ke cikin birane, ba na cikin karkara ba.
A ta bakin ta, ta ce wannan umarni ne daga Ofishin Shugaban Kasa.
Sannan kuma za a yi amfani da lambar asusun a ajiyar banki, wato BVN, a raba kudaden ga wanda ba shi da sama da naira 5,000 a asusun sa ba banki.
Tuni kuma wasu suka fara fitowa fili su na sukar yadda za a damka rabon kayan agaji ga gwamnatin jihohi.
Masu sukar wannan sabon tsari na ganin cewa za a saka siyasa a lamarin, yadda masu adawa ba za su samu ba. Kuma za a raba kudaden a matsayin tukuici ga ‘yan jagaliya.
Discussion about this post