Kasashen duniya 15 da basu da Coronavirus

0

Sakamako rahoton Wordometer ya nuna cewa har yanzu akwai kasashe 15 a duniya da ba su kamu da cutar coronavirus ba.

Yanzu an yi tsawon watanni biyu kenan tun bayan bullowar cutar inda a yanzu haka mutane sama da miliyan biyu na dauke da cutar, 127,587 sun mutu sannan 491,599 sun warke a duniya.

Kasashen da cutar ba ta bullo ba sun hada da Comoros, Lesotho, Korea ta Arewa, Tajikistan, Turkmenistan, Solomon Islands, Vanuatu, Federated States of Micronesia, Tonga, Marshall Islands, Palau, Tuvalu da Nauru.

Kasashen Comoros da Lesotho ne kasashen dake Nahiyar Afrika da har yanzu ba su samu bayyanar coronavirus ba.

NAHIYAR AFRIKA

Comoros kasa ce dake gabashin Afrika dake da mutane 865,000 a cikin ta.

Ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Comoros ya bayyana cewa rashin yi wa mutane gwajin cutar na daga cikin dalilan da ya sa har yanzu ba a samu labarin bullowar cutar a kasar ba.

Kasar Lesotho ta saka dokar hana walwala sannan ta rufe iyakokin kasar ta ganin cewa ita ce kasa mafi kusa da kasar Afrika ta Kudu.
Dokar hana walwala da Lesotho ta saka ya fara aiki ne tun daga ranar 3 ga watan Maris.

ASIA

Coronavirus bata bullo a kasashen Korea ta Arewa, Tajikistan, da Turkmenistan ba.

Korea ta Arewa ita ce kasar da ta fara saka dokar hana walwala da rufe iyakokin kasar ta ganin cewa tana kusa da kasar Chana inda cutar ta fara bullowa.

Korea ta Arewa ta rufe iyakokin kasar ta ne tun a ranar 21 ga watan Janairu sannan har yanzu dokar na aiki.

Kasar Tajikistan na da iyaka da kasashen Uzbekistan, Kyrgyzstan, China da Afghanistan wanda duk suna fama da cutar a kasashen su.

Bayanai sun nuna cewa Tajikistan ta dade kafin ta saka dokar hana walwala da rufe iyakokin kasar duk da cewa ta na kusa da kasashen da ke fama da wannan annoba.

AUSTRALIA

A yankin kasashen Solomon Islands, Vanuatu, Samoa, Kiribati, Federated States of Micronesia, Tonga, Marshall Islands, Palau, Tuvalu da Nauru na cikin kasashen da coronavirus ba ta bullo ba.

Samoa, Tonga da Kiribati sun saka dokar tabaci a kasashen su.

Sannan kasashen Federated States of Micronesia da Marshal Islands sun hana mutane yin tafiya a kasashen su.

Coronavirus ba ta bullo ba a kasashen Tuvalu da Nauru ba saboda ba su yawan samun baki dama can na shigowa kasashen.

Share.

game da Author