Duk da dai wata karin magana na cewa, “daji bai gama cin wuta ba, ba a yi wa burgu barka”, wannan ba zai hana a tabo bayani kan wasu kasashe 18 na duniya ba, wadanda har yau cutar Coronavirus ba ta bulla a cikin su ba.
Tashin farko dai ya kamata a san cewa Coronavirus ta kutsa kai kakaf din kasashen Turai, ba ta rage ko guda daya ba. Sannan kuma Nahiyoyin Amurka ta Arewa da ta Kudu, can ma babu kasar da Coronavirus ba ta shiga ta yi kamu ba.
Amma kuma har zuwa safiyar Alhamis akwai wasu kasashe cikin Nahiyar Afrika, Asia da Australia da har yau cutar ba ta dira ko bulla a can ba.
A Afrika, akwai kasashen Comoros Island, Lesotho, Malawi, Sao Tome da Sudan ta Kudu, wadanda har yau sai dai labarin cutar kadai su ke ji.
Comoros Island ya yi iyaka da kasashen Mozambique, Tanzania, Madagascar da Tsibirin Seychelles, wadanda tuni Coronavirus ta shige su, amma ba ta shiga Tsibirin Comoros ba.
Haka ita ma Lesotho ta hada iyaka da Afrika ta Kudu, wadda Coronavirus ta yi wa katutu. Cutar ba ta shiga Malawi ba, duk kuwa da cewa kasar ta hada kan iyaka da Zambia, Tanzania da Mozambique, wadanda duk sun kamu da cutar.
A Nahiyar Asiya, akwai kasashe irin su Koriya ta Arewa, Tajikistan, Turkmenistan da Yemen wadanda cutar ba ta kutsa can ba.
Turkmenistan ta hada kan iyakar kasa da Iran, Afghanistan, Uzbekistan da Kazakhstan da cutar ta yi katutu cikin su.
A Nahiyar Australia, Coronavirus ta kama kusan mutum 6,000, amma har yau ba ta kutsa Solomon Island ba da Palau, Tuvalu, Nauru, Kirbari, Micronesia, Vanuatu, Tonga da Marshal Island ba.