KARYA DOKA: ‘Yan sanda sun damke mutum 986 da suka karya dokokin coronavirus a Kaduna

0

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna, Umar MUsa Muri ya bayyana cewa jami’an sa sun damke masu laifi a fadin jihar har 986.

Muri ya ce dukkan su sun karya dokar zaman gida dole ne da kuma kin yin nesa-nesa da juna da aka saka a garin Kaduna.

Kwamishina Muri ya kara da cewa mutum 48 cikin wadanda aka kama, shugaban addini ne da kuma dillalan saida barasa, wato gidajen giya.

Ya ce dukkan su sun ki bin umarnin gwamnati sannan sun karya dokokin da ak gindaya na kiyaye wa daga yada coronavirus a al’umma.

A karshe ya ce baya ga wadannan an kuma kama, ‘yan bindiga, mahara, masu garkuwa da mutane, barayin cikin gari masu fasa shagunanan mutane da ‘yan ta’adda.

Share.

game da Author