KANO TA DAGULE: Masu cutar Coronavirus 3 sun yi layar zana cikin jama’a

0

Babban Jami’in Kwamitin Yaki da Coronavirus a Jihar Kano, Tijjani Hussaini, ya bayyana cewa wasu mutum uku da aka auna kuma aka same su dauke da cutar Coronavirus, sun sulele daga gidajen su, an rasa inda su ka yi.

Ya shaida PREMIUM TIMES cewa an Debi sinadaran jikim su domin a yi gwaji. Amma daga bisani sun canja adireshin su, kuma duk sun kashe wayoyin su.

Ya ce har yau ana ta kokarin gano inda su ka boye. Amma jami’an mu tare da jami’an tsaro da taimakon masu unguwa, su na ta kokarin gano inda su ka boye, domin a kamo su Kula a killace su.

Sai dai bai bayyana sunayen su ko unguwar da su ke ba. Amma dai ya ce tabbas mutanen yankin su duk su na sane da labarin arcewar da su ka yi. Kuma sun san ana neman mutanen su uku masu dauke da cutar.

“A cikin mutum 71 da aka samu dauke da cutar a Kano, mutum 3 sun tsere daga gidan su, kuma sun kashe wayoyin su. Ba a san inda suke ba har yau.

“Amma mun saka jami’an tsaro cikin lamarin ana ta kokarin kamo su a killace su.”

PREMIUM TIMES kuma ta bada lanarin korafin da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi, inda l ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da mawuyacin halin da jihar Kano ke ciki, wajen yaki da cutar Coronavirus.

Ganduje ya yi wannan kakkausan suka ne a ranar Litinin, lokacin da ya ke zantawa da wakilin BBC Hausa a Kano.

Ya ce halin da Kano ke ciki abin damuwa ne matuka, kuma abin tsoro. Daga nan ya yi korafin yadda Kwamitin Shugaban Kasa Mai Yaki da Cutar Coronavirus ya yo watsi da halin da Kano ke ciki.

Ganduje ya shaida wa BBC cewa hatta Shugaban Kwamitin sai da ya je Kano ya kwana, ya ga halin da ake ciki.

“Shi ma Ministan Harkokin Lafiya san halin da ake ciki a Kano.

“Amma yau kwanaki biyar ko shida kenan rabon da a yi gwaji a Kano. Saboda akwai matsalar karancin kayan gwaji. Ka san BA abu ba ne da za ka je kowace kasuwa ka sawo.

“Kuma duk mun sanar da su, sun san halin da Kano ke ciki. Tun farko ma sai da muka shaida musu cewa wurin yin gwaji guda daya ya yi kadan a hari babba kamar Kano. Amma ba su yi komai ba.”

Idan ba a manta Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce an dakatar da gwaji a Kano, saboda wasu masu aikin gwajin a Kano sun kamu da cutar.

Sannan kuma Shugaban Gwajin na Kano ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an dakatar da gwajin saboda rashin wasu kayan aiki kuma ana so a yi wa dakin gwajin feshin rigakafin kamuwa da cutar Coronavirus.

Jihar Kano ba fama da yawan mace-mace a kullum kusan kwanaki biyar a jere.

Yayin da wasu ke danganta yawan mace-macen da sagwangwaman Coronavirus, wasu kuma na ganin karancin asibitoci ne ya haddasa daina kula da masara lafiya a jihar, har suke mutuwa a gida.

Gwamna Ganduje na ci gaba da shan caccaka saboda zargin saka siyasa da yq yi a shirin yaki da Coronavirus a Kano, inda ya tsarma ‘yar cikin sa a cikin kwamiti.

Share.

game da Author