Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Umar Dambatta, ya ce kafafen sadarwa sun kasance kashin bayan ingantawa da rage yawan mutanen da ba su tu’ammali da tsarin banki a Najeriya.
Dambatta ya yi wannan bayani kamar yadda aka wallafa a shafin NCC na Twitter cewa, ya yi maganar lokacin da jami’an Gidauniya Bill da Melinda suka kai masa ziyara a hedikwatar hukumar.
“Mun gano irin muhimmancin da sadarwar Isar da sakonni ke da shi wajen inganta harkokin tattalin arziki, shi ya sa mu ka yi kokarin gano duk inda ake samun cikas sadarwa a ayyukan raya kasa a fadin Najeriya.”
Dambatta ya kara da cewa an bai wa kamfanoni lasisin janyo wa daga bakin tashoshin ruwa har zuwa cikin kasa a fadin kananan hukumomi 774, domin inganta sadarwa.
Ya ce idan aka bai wa kamfanonin sadarwa iznin bunkasa ayyukan su a cikin kasa, hakan zai inganta harkokin bunkasa hada-hada a hannun jama’a masu karamin karfi.
Dambatta ya akalla akwai mur milyan 35 d ba au amfani da tsarin sadarwa a kasar nan, wanda hakan kuma kan kawo cikas ga hada-hadar kudade, musamman wajen kasa rage wadanda ba su iya hada-hadar banki a kasar nan.
Ya ce samar da wadatar kafafen sadarwa a yankunan karkara zai kasa sa jama’a ko’ina su rungumi tsarin hada-hadar kudi ta zamani, ta yadda za a iya cika burin ganin an samu kashi 80 bisa 100 na al’umma sun rungumi shirin amfani da sadarwar zamani wajen hada-hadar kudade.
Ya kuma yi bayanin yadda Babban Bankin Najeriya, CBN ya shigo da tsarin hada-hadar kudi na kai-tsaye, wato Mobile Banking Services, domin inganta tsarin a ko’ina cikin fadin kasar nan.
Tun a cikin shekara ta 2010 ce aka yi kirdado da kintacen za a rage mutanen da ba au mu’amala da banki daga kashi 46.3 zuwa kashi 20 daga shekarar zuwa 2020.
Daya daga cikin wakilan Bill da Melinda Gates Foundation, Abiodun Jagun, ya ce Gidauniyar ta nemi yin hadin-guiwa da Gwamnatin Tarayya domin a kara samun shigar dimbin jama’a a cikin harkar hada-hadar kudade.
Babban abin da ke ci wa shirin ‘Financial Inclusion’ tuwo a kwarya, shi ne rashin damar yin hada-hadar banki ga mutane marasa karfi, masu karancin samun kudaden shiga. Wannan matsala kuwa kan hana su samun damar fita daga cikin kangin talauci da kuncin rayuwa.
Idan aka samu nasarar da irin wannan shirin ta inganta hanyoyin sadarwa har a kananan hukumomi kuwa, to samun damar hada-hadar kasuwanci da kudade ta kafafen zamani zai yi wa jama’a masu karamin karfi saukin gaske.