Kaduna ta kama matafiya cunkushe da dabbobi a tireloli za a sulalo dasu cikin gari daga Kano

0

Jami’an tsaro sun kama wasu tireloli da aka cunkusa dabbobi, mutane da babura za a sulalo da su cikin garin Kaduna daga Kano.

Su dai wadannan Tireloli sun taho daga Kano ne kamar suna dauke da kayan abinci ne, ashe mutane da dabbobi ne cunkushe a ciki za a kawo su Kaduna a boye.

Ba su yi sa’ar wuce wa jami’an tsaro suka kama su.

Idan ba’a manta ba, a ranar litinin ma Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, na jihar Kaduna Samuel Aruwan tare da jami’an tsaro sun kama wasu tireloli dankare da mutane daga Kano za a kawo su garin Kaduna a boye.

Kwamishinan da Jami’an Tsaro sun tare wadannan motoci ne a Kauyen Sabon Gida dake iyaka da Jihar Kaduna da Kano.

” Ko da muka kama tirelolin, mun umarce su su bude wuraren ajiyan kaya, budewar su ke da wuya sai muka iske mutane dankare a ciki a kwankwance za a kawo su garin Kaduna. Abinda yayi mana dadi shine ba su kai ga shigowa gari ba. Duk mun ce su juya su koma inda suka fito.

” Haka kuma bayan su mun fatattaki wasu fasinjojin da yawa duk mun saka sun koma garuruwan da suka fito.

Bayan haka Aruwan ya ce sun garzaya iyakar jihar da Katsina, Iyakar Kudan da Danja. Sannan kuma kwamishinan sun fatattaki wasu da suka fito cin Kasuwa a garin farakwai.

Jami’an tsaro sun damke wasu da dama da tuni har ta mika su ga hukumomi domin a yanke musus hukuncin karya doka.

Idan ba a manta ba gwamnatin Kaduna ta saka sabbin dokoki na hana walwala a jihar da ya hada hukunta wanda ya karya doka nan take.

Sannan kuma harda hukunta wadanda suka karya dokar shigowa garin Kaduna.

” Duk matafiyin da ya shigo Kaduna da gangar, za a killace shi na kwanaki 14, ko kuma ya koma inda ya fito. Sannan kada ya dauka za a killace shi don nishadi ne.

” Duk motar da aka kama shikenan mai ita zai rasa ta har abada domin zai koma mallakin gwamnati. Sannan duk kamfanin dake da mallakin wannan mota zai fuskanci hukunci. Domin za a kai shi kotu sannan za a kwace lasisin yin aiki a jihar Kaduna. Shima direban wannan mota sai ya biya tara ko a daure shi.

Share.

game da Author