Fadar Shugaban Kasa ta maida wa sanata Ali Ndume da kakkausar martani inda ta karyata korafin da ya yi cewa ana tafka harkalla a rabon tallafin agaji da gwamnatin tarayya take baiwa ‘yan Najeriya.
Sanata Ali Ndume ya zargi Kwamitin Rabon Kayan Tallafin Rage Radadi Lokacin Coronavirus, wanda ke karkashin Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Umar, da tabka almundahana, harkalla da rub-da-ciki.
Ndume, wanda ke wakiltar Mazabar Sanatan Barno ta Kudu, ya ce idan dai ba Shugaba Muhammadu Buhari ya na so a kifar masa da dan sauran kima da mutuncin sa da suka rage a cikin yashi ba, to ya gaggauta kwace rabon kudi da kayan agaji daga hannun kwamitin da Sadiya Farouq ke shugabanta.
Ya ce kuma shi ba zargin Minista din ko wasu ‘yan kwamitin ya ke yi ba. Duk maganar da ya ke yi, ya na da tulin hujjoji.
“Mu na ci gaba da samun korafe-korafe a kan yadda kwamitin rabon tallafi ke harkalla. A rage wa Shugaba Buhari ya rusa kwamitin tun kafin su rusa masa sauran mutuncin sa.”
“In banda harkalla, ya za a ce Jihar Zamfara inda Minista Sadiya ta fito, za a ce an yi wa fakirai 1, 341,153 rajista a gidaje 291,629, ya zuwa 20 Ga Maris.
“Amma Sokoto gidaje 3,347 kadai, kuma mutum 18,435 kacal. Barno gidaje 7,130, Kula mutum 33,728 kacal.
“Mu na kwararan hujjoji da suka tabbatar da cewa sun rika tattaro sunayen bogi. Mutum daya sai ta rubuto sunayen dubban mutane, ya hada baki da dibgaggun jami’an banki a kirkirar musu lambar BVN. Kuma idan aka yi bincike za a tabbatar da haka.
“Sun maka sunayen masu dafa musu abinci, na direbobin su, na dangin su, na dangin boyi-boyin su da ka sauran masu yi musu hidima. Wai su ne tantiran fakiran da su ka cancanci a raba wa tallafin.” Inji Ndume.
Sai dai kuma fadar shugaban kasa ta maida masa da kakkausar martani inda ta ce ya bayyana hujjojin sa ko kuma ya yi wa mutane shiru.
Garba Shehu da ya saka hannu a wannan takarda ya ce gararamba kawai Ndume yake yi amma bashi da hujjoji. Idan kuma yana da su ya fito ya bayyana sunaye ba ya rika jifa a kasuwa ba.