Gwamnatin Jihar Filato ta fara binciken yadda wasu ko wani ya fallasa sakamakon gwanin cutar Coronavirus, wanda aka gudanar a Cibiyar Gwajin Coronavirus da ke Cibiyar Binciken Cututtukan Dabbobi da ke Vom.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Dan Manjang ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a ranar Lahadi.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa a ranar Alhamis ce aka rika watsa wani sakamakon gwajin Coronavirus, wanda kuma ya tabbatar da cewa wanda aka auna din ya na dauke da cutar.
An rika watsa sakamakon a soshiyal midiya, tun kafin hukuma ta bayyana shi daga bakin ta.
Fallasa wannan sakamakon tun kafin Hukumar NCDC da Gwamnatin Filato su bayyana shi, ya harzuka gwamnatin matuka.
Wanda ke dauke da cutar dai shi ne na farko da aka samu dauke da cutar a jihar Filato, kuma daga jihar Kano ya je Jos, a ranar 17 Ga Afrilu.
Kwamishina Manjang ya ce rashin mutunci ne da kuma rashin bin ka’idar aikin likita da karya doka aka yi har aka fallasa sakamakon, wanda hakan ya ce zai iya sa wanda ke dauke da cutar ya fuskanci tsangwama, kyara da kyamata a cikin al’umma.
Kwamishinan ya yi tir da abin da ya faru, kuma ya bai wa jama’a hakuri, ganin cewa wannan kasassaba za ta iya kawo tawaya da rashin yin amanna ga aikin gwajin da kuma rashin bada amana ga su jami’an yin gwajin.
Ruben Ocholi, wanda shi ne Shugaban Riko na Cibiyar ta NVRI da ke Vom, Jos, ya nuna rashin jin dadin abin da ya faru.
Ocholi ya ce Cibiyar sa wuri ne da ake bin ka’idar aiki ka’in da na’in. Daga nan sai ya yi kira ha Gwamnatin Jihar Filato ta bincika kuma ta kama wanda ko dukkan wadanda ke da hannu wajen fallasa sakamakon gwajin.
Discussion about this post