Wani abu da na kwana da shi a zuciya ta, na kwana yana min radadi da ciwo shine yadda naji wani maigadi ya tattago cutar coronavirus tun daga Legas cikin motar haya zuwa garin Kaduna sannan ya ci gaba da al’amurorin sa na kwanaki kafin aka gano bashi da lafiya kuma yana dauke da cutar coronavirus ne.
Dole hankalin mutane ya tashi matuka, domin kuwa Allah kadai yasan irin yawan mutanen da yayi mua’mula da su tun daga Legas da kuma wadanda ya cakudu da a Kaduna kafin ya kwanta rashin lafiya.
Ga shi kuma mutanen mu dama akwai taurin kai. Da yawa daga cikin su basu yarda cewa ma akwai cutar ba duk da daruruwan da ake sanarwa sun kamu har da manya da gwamnoni, duk da haka basu yarda ba.
Idan aka bari coronavirus ta yadu cikin talakawa, an shiga uku, Daga Aisha Yusufu
Abin da zai bakanta maka rai shine yadda za ka ga mutane na walwala cikin jama’a a cunkushe babu ruwan su. Kai baka san wancan daga ina yake ba, shi bai san wa ka tabo ba duk a gwarmaya wuri daya babu abinda ya dada mutum da kasa. Ga kuma taurin kan tsiya.
Tabbas akwai cutar coronavirus kuma ba ta da magani har yanzu. Kasashen da muke takama da su a duniya, muke bugun kirji da su cewa suna da karfin arziki da kiwon lafiya duk sun fada cikin halin ha’ulai. Cutar ta fi karfin su kowa yana ta kai ne yanzu.
Mu a Najeriya, gwamnatin mu na kokarin ganin cutar bata kai ga an shiga yanayin kowa yayi ta kan sa ba. Amma kuma mutane da wasu gwamnatocin jihohin na nuna halin ko in kula.
Da mutane za su hakura a iya taro wannan cuta a inda yake ayi wa wadanda ke da ita magani kafin ta yadu da yafi zama mana sauki maimakon a rika yi wa maganar sakainar kashi ana cewa ba gaskiya bace tutar.
Yanzu dole mutanen Kaduna musamman unguwan da wannan mutum yake zaune su mika kansu da kansu a yi musu gwaji domin sanin matsayin su. Sannan kuma gwamnati ta bi duk inda ake zaton mutumin nan ya garzaya a killace mutane.
Yanzu ne Najeriya ke bukatar zaman gidan dole domin talakawa da wasu masu taurin kai sun fara tallar cutar da karfi da yaji.
A rika nesanta kai daga taruwa cikin jama’a, sannan a maida hankali wajen yawita wanke hannaye, da goge hannu da man tsaftace hannaye, kuma a rika tsaftace wuraren zama.
Allah ya bamu Lafiya, Amin.