Daruruwan Almajirai ne aka maida jihar Jigawa daga garin Kano a makon da ya gabata.
Gwamnatin Kano ta ce ta yi haka ne saboda kare yaran daga kamuwa da cutar Coronavirus da ake fama da ita a duniya.
Almajirai dake gararamba a titunanan kasarnan basu samun kula sannan wasun su basu ma san ma abin da suka yi ba a rayuwa.
Gwamnatocin Arewa sun yanke shawarar maida duka almajirai dake wasu jihohi ba jihohin su ba a fadin yankin.
Discussion about this post