Hana Sallah a masallatai ba shine kadai mafita ba wajen hana yaduwar KWARONABAIRUS (COVID-19), Daga Anas Ɗansalma

0

Annobar cutar kwaronabairus (COVID-19), annoba ce da ta tilasta wa duniya gaba ɗaya durƙuso a kan guiwowinta bayan gaza samun wata sahihiyar hanya ta yin magani ko ma yin riga-ƙafinta. Wannan ta sa mahukunta dagewa da tashi kai tsaye wajen ganin an bi matakai da masana, musamman na ƙasar Sin (China) suka bayar kuma suka yi amfani da su wanda ake ganin ya taimaka musu, musammman a garin Wuhan na ƙasar Sin ɗin wajen kawar da wannan ƙwayar cuta. Amfani da wannan hanyoyi haƙiƙa abu ne mai kyau, saidai, a ƙasashen Musulmi waɗannan matakai, musamman na zaman gida sun ci karo da wasu abubuwa na addini wanda hakan ya bar baya da ƙura.

Tun bayan gano hanyoyin yaɗuwar wannan cuta da ya haɗa da: taɓa wurare da ke ɗauke da ƙwayoyin cuta (touching spaces), rashin samun tazara a tsakanin mutane na ƙalla mita ɗaya ko biyu (social distancing) wanda yin hakan ke taimakawa wajen nisantar mai tari da atishawa daga kamuwa da ita. Har’ila yau, saka takunkumi (face mask) na taimaka wa wanda ya kamu da cutar da ma wanda bai kama da ita ba wajen daƙile yaɗuwarta da kuma kamuwa da ita. Ga batun wanke hannu wanda tuni Musulinci saboda wayewarsa ya koyar da mu muhimmancin wanke hannu domin kawar da datti (washing one’s hands) tun kafin taɓa komai. Wataƙila ƙari a kan hakan bai wuce amfani da sabulu (soap) da kuma sanitaiza (sanitiser) ba. Na ƙarshe kuwa cikin muhimman matakai na kariyar daga wannan annoba shi ne keɓance kai ga matafiya da kuma zaman kulle a gidajenmu da dai sauransu.

To, abin tambayar shi ne ko hana yin salloli a masalatan kamsussalawat ka iya hana ko rage kamuwa da wannan cuta? Shin wannan ne masalaha? Amsa ta farko dai, a ra’ayina na Musulmi kuma mai neman ilimi wannan ba shi ne mafita ga wannan larura ba kuma babu wata masalaha saboda dalilaina da zan bayyana a ƙasa.

La’akari da irin kiraye-kiraye da hukumomin gwamnati da shuwagabanni na musulinci, musamman daga fadar mai Alfarma Sarkin Musulmi na ba da umarnin al’umma su ƙaurace wa masallatai tare da ɗabbaƙa sallah a gidaje. Ba na ja kan cewa cakuɗuwa da mutane wata hanya ce ta kamuwa da wannnan cuta, saidai fa wacce iriyar cukuɗuwa muke magana a kai? Kuma meye bambancin TARUWA a masallatai da kuma CAKUƊUWA a sauran wurare na turawar mutane? Da farko dai a mutane sukan taru a wurare da yawan gaske da suka haɗa da: kasuwanni da makarantu da gidajen kallon bal (ƙwallo) da wuraren wasa ƙwallon ƙafa (stadium) da sauran filaye da wuraren shaƙatawa da kulob-kulob da wauraren tarukan siyasa da kuma masallatai da coci-coci da sauran tatattaki na tarukan addini.

Tsarin haɗuwa a masallatai ya bambanta da sauran gaba ɗaya wuraren da na ambata domin kuwa masallaci ba cakuɗuwa ake yi ba, jeruwa ake yi kuma da za a ce ɗaya bayan ɗaya ake so kowa ya shiga masallaci, musamman na unguwnani, to da ba za a samu wata matsala ba, idan ka kuma kwatanta shiga kasuwanni ga misali, abin da ya faru a Kano a ranar 23 ga watan Afrilu, 2020, inda mutane suka shiga kasuwanni domin siyayyar kayan azumi sakamakon sake garƙame gari da za’ayi. Kowa shaida ne na yadda mutane suka yi watsi da dokokin da masana suka shinfiɗa wajen samun kariya daga kamuwa da wannnan cuta. Wane tsari gwamnatoci suka yi? Ba ma a Kano kaɗai ba, har ma da sauran kasuwanni na sauran jihohi?

Shawarata ga hukumomi shi ne su tuna cewa addinin Musulinci yana da tsari. Sallah ga duk wani Musulmi wajibi ne wanda hadisai da tarihi ya tabbatar da saboda wajibcin sallah, lallai ne a gabatar da ita ko da kuwa a yayin jihadi (YAƘI) ne. Idan malamai za su yi fatawa, na san ba za su gaza tabbatar da cewa yanayin yaƙi ya fi na wannan halin annoba ta kwaronabairus da muke ciki ba. Kamata ya yi gwamnatoci su kira malamai da limamai ta hanyar masarautu da ke garuwa a Nijeriya tare da samar musu da takunkumi da sanitaiza da kuma wayar da kansu domin tabbatar da an samar da tsari na ƙayyade adadin mutanen da ya kamata su yi sallah a kowanne masallaci domin tabbatar da an samar da tazara a tsakanin kowanne mutum a masalatai kamar yadda ƙasashe da yawa na Larabawa suke gabatarwa. Wajibi ne kuma limamai su tabbatar da cewa kafin shigowar kowanne mutum masallaci, to ya zama dole ya wanke hannunsa da sabulu da kuma amfani da sanitaiza a yayin fitowa domin komawa gidajenmu. Gwamnati kamata ya yi ta fara feshin maganin karya garkuwar wannan cuta a kowanne lungu da saƙo na kowacce jiha tare da haɗa kai da masu hannu da shuni wajen ganin an samar da waɗancan kayayyaki a masalatai kamar yadda na ambata a baya.

A ƙarshe, gwamnatoci ya kamata su mai da hankali ne ga samarwa da talakawa tallafin na kayan abinci da kuma wadatattun likitoci a asibitoci da maguguna kyauta ko kuma cikin farashi mai rahusa domin samun haɗin kansu wajen kawar da wannan cuta gaba ɗaya kafin al’umma su yi mata boren yunwa su yo waje da gudu saboda tsananin takura ta babu da za ta addabe su. Yana da kyau gwamnati ta yi koyi da gwamnatocin ƙasashen da ke ba su tallafi na kuɗaɗe da kayan lafiya ta fuskar jinƙan talakawansu.

Abin kunya ne izuwa yanzu akwai jihohi kamar Kano da babu kayan aikin gwaji na wannan cuta da kuma wasu jihohin da ba su da na’urar numfasawa (ventilators) da ma a wasu wuraren, babu wuraren killace mutane masu wannan cuta da za a kira ingantacce. A maimakon yaƙi da batun kar a fita sallah ko coci-coci, kamata ya yi gwamnati ta warware waɗancan abubuwa domin samar da yanayi mai kyau na yaƙar annobar kwaronabairus (COVID-19) tare da ‘yaƙar yunwa kafin talakawa su fara satar kayan abinci don su samu su rayu.

Daga Anas Ɗansalma

Share.

game da Author