Gwamnonin Najeriya sun yi kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar hana walwala da ya saka a musamman Jihohi biyu da babban birnin tarayya.
Hakan ya biyo bayan ganawa da kungiyar ta yi da mataimakin shugaban Kasa, Yemi Osinbajo a wannan mako.
Gwamnonin sun ce za a iya ci gaba da hana walwalan jama’a musamman daga wannan jiha zuwa waccan amma a bude gari kowa ya iya wataya wa.
Sai dai kuma sun ce za ci gaba da horas da mutane da nuna musu illar cunkoso a tsakanin su da kuma amfanin saka takunkumin fuska da safar hannu sannan kuma da wanke hannaye.
Takardar waddda suka aika wa ofishin Sakataren Gwamnatin Najeriya, sako ga Buhari.
Wannan na daga cikin kukan ga gwamnoni suka mika wa shugaba Buhari ganin cewa ranar Litinin ne wa’adin dokar zaman gida dole a wasu jihohi zai ciki.
Sai dai kuma masu yin fashin baki a harkar wannan annoba sun yi kira ga gwamnatocin su yi takatsantsan da sakin mutane bakatantan ba tare da an samar da kariya musu ba.
A kullum Najeriya na samun karuwar wadanda suka kamu da cutar ne, ba raguwa ba ballantana ace wai an janye dokar kwata-kwata a jihohi da kasa baki daya. Wannan hali da ak shiga san an bi a hankali. Kuma mutane sun kiyaye matuka.