Gwamnatin Tarayya ta sake kaddamar da rabon Tradermoni a Katsina

0

Gwamnatin Tarayya ta sake kaddamar da rabon kudin Tradermoni na naira 10,000 ga duk mutum daya, wadanda aka raba wa mutum 5,000 a matsayin lamuni a Katsina.

Shirin wanda aka kaddamar da shi a ranar Asabar a Katsina, an bayar da lamunin ne a matsayin bashi ba mai ruwa ba, domin su farfado daga radadin kuncin da aka shiga, saboda annobar Coronavirus.

Ya zuwa ranar Asabar, 18 Ga Afrilu dai akwai mutum 9 da suka kamu da cutar Coronavirus a jihar Katsina.

Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq ce ta kaddamar da shirin, a karkashin wakilcin Mataimakin Daraktan Agajin Gaggawa, Abubakar Sulaiman.

Sulaiman ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin a raba tallafin lamunin domin a rage wa jama’a radadin talauci.

Ya kuma ce cikin wadanda za a raba wa kudaden har da marasa galihu da kuma nakasassu.

Makonni uku da suka gabata ne Buhari ya bada umarnin a raba kudaden tallafin lamuni na watanni uku na tsarin Tradermoni, Marketmoni da kuma Farmermoni.

Ya kuma sa a raba sauran shirin lamunin da suka jibinci gwamnatin tarayya ga jama’a, domin a rage kuncin rayuwa.

Za a iya bai wa marasa galihu lamunin naira 15, 000, idan ya biya bai cinye kudin ba, za a iya kara masa har zuwa naira 100,000.

Marketmoni kuma za a iya bai wa karamin dan kasuwa lamunin daga naira 10,000 har zuwa naira 350,000 in dai ba ya na biya, ba ya cinye kudin.

Minista ta ce mutane 130,455 ne suka amfana da tsarin a jihar Katsina.

Share.

game da Author