A ranar Laraba ne gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce gwamnati za ta yi amfani da maganin zazzabin cizon sauro wato ‘Chloroquine’ da ‘Zithromax’ domin warkar da cutar Covid-19 a jihar.
Gwamna Bala ya ce wadannan magunguna ne ya yi amfani da su har ya warke a lokacin da ya kamu da cutar.
Mohammed ya umurci ma’aikatan kiwon lafiya dake jihar su fara amfani da wadannan magunguna domin warkar da masu fama da cutar a jihar.
Ya ce saboda ana amfani da wadannan magunguna ne ya sa har yanzu babu wanda aka rasa a jihar.
“Jikin mu ya saba da wadannan magunguna domin ko zazzabi ya kama mutum za ka iya sha domin samun sauki. Sannan a maimakon mu biye wa abin da bature ke fada na rashin maganin cutar gwara mu yi amfani da abin da muke da su kawai.
Tun da cutar Covid-19 ya bullo ma’aikatan kiwon lafiya ke ta korafi kan ingancin maganin wajen warkar da cutar a duniya.
Yayin da wasu bangarorin duniya ke cewa maganin na warkar da cutar, Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da wasu kwararrun likitoci sun ce ba su da tabbacin ko maganin na iya warkar da cutar Covid-19.
Sun ce za su gudanar da bincike a kan maganin domin yawan amfani da maganin na iya yi wa jikin mutum illa.
Kin saka dokar zaman gida dole
Mohammed ya bayyana cewa gwamnati ba za ta saka dokar zaman gida dole ba a jihar a matsayin matakin hana yaduwar cutar coronavirus.
Ya ce wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin gujewa wa kamuwa da cutar, hana tarurrukan mutane ne kawai matakan dakile yaduwar cutar da gwamnati za ta dauka a jihar.
Bayan haka gwamnan jihar ya ce domin karfafa yin gwajin cutar a jihar gwamnati zata gina nata wurin gwajin a jihar.
Ya ce a cikin kwanaki 10 gwamnati zata gina wurin gwajin cutar a jihar wanda zai rika iya yi wa mutum akalla 1000 gwajin cutar a rana daya.
“Muna mika gidiyar mu ga gwamnatin tarayya da Hukumar raya yankin Arewa maso Gabashin kasar nan kan goyan bayan da suka nuna mana a jihar.
“Duk da haka idan gwamnati ta samu wasu kudaden za ta kara gina wani wurin gwajin cutar a Azare domin kusancin garin da jihohin Kano, Jigawa da Barno dake fama da cutar.
Sannan ya kara da cewa jihar na da asibitoci 4 da ta bude kuma ta zuba na’urori domin kula da mutanen da suka kamu da cutar a jihar.
A tsakanin kwanaki biyu jihar ta samu karin mutun 18 da suka kamu da cutar.
Yanzu mutum 1728 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 307 sun warke, 51 sun mutu.
A yanzu dai mutum 29 ne ke dauke da cutar a jihar inda daga ciki am sallami 6, 23 na Kwance a asibiti.