Mahukuntan Sojojin Najeriya sun bayyana nasarar gwabza yaki da Boko Haram, inda suka kashe ‘yan ta’adda 105 a jihar Yobe.
Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya fitar da takardar sanarwa ga manema labarai a Damaturu cewa, an kashe mahara 105 a bayan garin Buni Gari, wanda ba ya da nisa da Bataliyar Soja ta 27 da ke Buni Yadi. A can ne kuma Makarantar Musamman Ta Sojoji Kwararru ta ke.
Rundunar Operation Lafiya Dole, Bangare ta 2 da ke karkashin Burgediya Janar Lawrence Araba ne suka yi wa Boko Haram wannan ragargazar, bayan da aka ba su labarin da ya yi sanadiyyar yi wa Boko Haram/ISWAP din ragargaza sosai.
Rahoton ya ce Buratai ya yi murna sosai da wannan gagarimar nasara da aka samu, yayin da kwamandan ya bayyana masa gwagwagwar da sojojin suka yi har suka yi wa Boko Haram 105 luguden wuta zuwa barzahu.
Buratai ya kai ziyarar ce ranar Lahadi, inda aka yi masa wannan babban albishir, wanda aka ce ya sa shi farin ciki.
“Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya na jinjina wa Batiliyar Sojojin da suka yi nasarar kashe Boko Haram 105 a Buni Gari, cikin Karamar Hukumar Gujba, a Jihar Yobe, a ranar 18 Ga Afrilu, 2020.
“Buratai ya fara yada zango ne a wani asibitin sojoji a Damaturi, inda ya duba lafiyar wasu sojoji biyu da aka ji wa ciwo a gumurzun Buni Gari. Daga can kuma ya duna wadanda ke wurin tuni su na jiya.
“Daga nan ya zarce Makarantar Zaratan Sojoji, inda Kwamanda Adaba ya yi masa bayanin yadda rundunar sa ta yi wa Boko Haram raga-raga.
Adaba ya ce sojojin sa sun kwato ganimar manyan makamai daga Boko Haram, wadanda suka hada da manyan bindigogi da sauran su.