GANGAR DANYEN MAI A DALA 12: NNPC ta ce farashin zai sake farfadowa

0

Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Kasa (NNPC), Mele Kyari, ya bayyana cewa ba za a karaya ba, ya san ba da dadewa ba farashin gangar danyen man fetur zai sake tashi daga mummunar faduwar da bai taba yi ba.

A yanzu dai ana sai da gangar danyen mai samfurin Bonny Light, wanda Najeriya ke hakowa dala 12 zuwa dala 13 kacal.

A tattaunawar da Mele Kyari ya yi da PREMIUM TIMES, ya ce duk da dai abin damuwa ne matuka, to tabbas ya san man zai sake tashi ya sake saida kan sa da darajar sa.

Duk kokarin da Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Danyen Mai (OPEC) ta yi na sasanta kasashen Rasha da Saudiyya da kuma amincewa kasashen su rage yawan man da suke hakowa a kullum da ganga milyan 10, hakan bai sake farfado da farashin danyen mai a duniya ba.

A yanzu dai farashin gangar danyen mai ko kadan bai kai adadin kudin da ake kashewa wajen hako ganga daya ba.

Cikin wannan watan ne Gwamnatin Tarayya ta soke kasafin kudaden 2020 saboda faduwar farashin danyen mai.

Sannan kuma a karshen Maris Mele Kyari ya ce idan farashin danyen mai ya kara faduwa kasa warwas, to Najeriya za ta daina hakowa, domin hakowar asara ce.

A karshen watan Maris, PREMIUM TIMES ta buga bayanin da Mela Kyari ya yi, inda ya ce Najeriya ta kusa daina hako man fetur saboda Coronavirus

Faduwar farashin danyen man fetur a duniya na daf da tilasta wa Najeriya dakatar da hako danyen mai har sai yadda hali ya yi.

A ranar Litinin da ta gabata, an dibga asarar farashin gangar danyen mai, ta yadda farashi a Kasuwar Hada-hadar Turai ta ICE Futures Europe Exchangr, ya kara faduwa warwas daga dala 25.82 kowace gangar danyen mai, ya sake raguwa da dala 1.16, wato zuwa dala 24.68 kenan na kowace gangar danyen man fetur a ranar Juma’ar da ta gabata.

‘Mun Bani Mun Lalace’ -Shugaban NNPC

Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Fetur (NNPC), Kyari, ya nuna matukar firgita dangane da faduwar farashin danyen man fetur.

Ya nuna cewa matsawar farashin ya sake yin kasa, ya ragu da ko da dala 3 ce daga yadda ya ke a yanzu, to Najeriya ba ta da wani zabi sai dai kawai ta daina hako mai, har sai yadda Allah ya yi.

“Idan har farashin gangar danyen mai ya kara yin kasa, ya koma dala 22 kowace ganga, to kasashen irin su Najeriya sai dai su zauna, su daina hako mai, domin ko an hako din ma asara ce mummuna kawai za a dibga.

“Babbar matsalar mu ita ce Najeriya na cikin sahun kasashe masu hako danyen man fetur da tsadar gaske. Ana kashe dala 15 zuwa 17 wajen hako kowace gangar danyen mai daya tal.

“To kenan idan har farashi ya fadi warwas daga dala 32 ko 30 zuwa dala 22, ai ba ka ma bukatar jiran sai wani malamin duba ya shaida maka cewa asara ka ke tabkawa idan ka ci gaba da hako danyen mai.

” Kasashe irin su Saudiyya da Iraq duk za su iya ci gaba da hako danyen mai, ko da ya kara karyewa da dala 8, Saudi za ta iya hakowa ta ci riba.

“Iraq za ta iya hakowa kuma ta ci riba, ko da ya kara raguwa da dala 5. Saboda su duk ba su kashe makudan kudade wajen hako danyen mai, kamar yadda kasashe irin Najeriya ke kashewa.”

Kyari ya danganta wannan gagarimar matsala ce da annobar cutar Coronavirus da kuma takun-sakar yakin danyen man fetur da ake yi tsakanin kasar Rasha da kuma Saudi Arabiya.

Ya zuwa yau dai ba a sani ba, ko Najeriya ta fara tunanin dakatar da hako danyen mai din, ganin cewa farashin sa bai kai dala 25 ba.

Share.

game da Author