Ganduje ya musanta rahotan mutuwar mutane 70 a Kano

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya karyata rahotannin da aka rika yruwaitowa cewa wai mutane sun yi ta mutuwa a Kano kamar kaji.

Da yake hira da tashar Channels, ranar Alhamis ya ce babu wannan babu shi domin gwamnati ta gudanar da bincike a wannan makabarta da aka ce mutum 70 sun mutu an bizne su.

” Mun gano mutum 13 ne suka rasu aka bizne a wannan makabarta, amma kuma gwamnati na ci gaba da bincike. Jaridar Daily Trust ta shirga wa mutane karya ne ruwaito cewa da ta yi wai mutum akalla 150 sun rasu a cikin kwanaki kadan.

Ganduje ya ce Kano na ci gaba da yi wa mutane gwajin cutar coronavirus a ko-ina a fadin jihar. Kuma gwamnati ta maida hankali wajen ganin ba a yada cutar ga musamman karkara ba.

Idan ba a manta ba Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an dakatar da gwajin masu cutar Coronavirus a Kano ne saboda wasu masu gwajin sun kamu da cutar a dakin da su ke yin gwajin.

Ehanire, wanda ya yi wannan bayanin da yammacin Ladaba, ya ce an kuma fuskanci karancin sinadarai da kayan aikin gwajin, wanda hakan ya sa tilas aka dakatar na wani dan takaitaccen lokaci.

“Rahotanni sun tabbatar an samu karancin kayan aiki musamman kayan kariyar da jami’an kiwon lafiya ke sakawa da daurawa. Kuma an samu karancin wasu sinadarai. Amma dai a yanzu duk mun tura musu kayan.

” Wasu masu aikin gwajin sun kamu a dakin da ke yin gwajin. Hakan ya sa tilas aka gaggauta rufe dakin gwajin, daga baya aka je aka yi masa feshin tsarkakewa daga. cutar Coronavirus.”

Ehanire ya ce rufewar ta wani dan takaitaccen lokaci ce, kuma tuni an ci gaba da aikin gwajin, saboda an aika musu da dukkan kayan aikin da ake bukata.

PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa ana a cikin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ake gwajin a wani dakin gwajin cututtuka (laboratory).

Can ne kuma ake kai gwaje-gwaje ana aunawa da jihohin Arewacin kasar nan da dama.

Share.

game da Author