Fassarar Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari kan karin kwanakin zaman gidan makonni biyu

0

1. Ya ‘Yan Najeriya

2. A jawabi na na farko da na yi, na umarci al’ummar Jihohin Lagos, Ogun da Babban Birnin Tarayya Abuja su zauna gida tsawon makonni biyu, wanda aka fara daga ranar Litinin, 30 Ga Mayu, 2020.

3. Wasu Gwamnatocin Jihohi da yawa kuma sun yi amfani da wannan salon doka a jihohin su.

4. A matsayin mu na shugabannin da ku ka zaba, mu na sane da cewa wannan tsatstsauran mataki da muka dauka zai jefa ku cikin kunci da takura, kuma zai jefa iyalan ku da yankunan ku.

5. Sai dai kuma wannan sadaukarwa da ku ke yi, ta zama tilas domin mu samu mu takaita kuma mu dakile tare da hana cutar Coronavirus kara fantsama a cikin jama’a ta yadda za mu ceci dimbin rayukan mutane.

6. Makasudin daukar wadannan matakai shi ne a hana cutar yaduwa tare da samar da yanayi, lokaci da kuma kudaden yin amfani da Su wajen daukar dukkan matakan da suka kamata a dauka.

7. Mun gamsu sosai dangane da yadda jama’a suke bin umarnin kiyaye ka’idojin kauce wa kamuwa da Coronavirus. Mu na godiya sosai da wannan sadaukarwar ceton juna da ake ci gaba da bayarwa.

8. Zan yi amfani da wannan dama na gode wa Sarakunan Gargajiya, Kungiyar Kiristoci ta Kasa, Majalisar Kilin Addinin Musulunci a kan gagarimar gudimmawar da suke kan bayarwa.

9. Ina kuma gode wa kan gudummawar da wasu masu kishi su ka bayar, su da wasu kamfanoni da kungiyoyi da kuma abokan mu.

10. Ina kuma gode wa kafafen yada labarai da sauran masu fadakarwa domin Jan hankalin yadda za a rika daukar matakan hana kamuwa da cutar Coronavirus.

11. Mun samu nasarar cimma abubuwa da dama a wannan lokaci sakamakon gudummawa da goyon bayan da muke samu.

12. Mun samu nasarar aiwatar da wasu tsare-tsaren kula da lafiya da suka hada da gano wadanda ake zargin sun kamu, yin gwaji da kuma killace wadanda ke dauke da cutar.

13. Ya zuwa yau mun gano akalla kashi 90 bisa 100 na wadanda aka dukufa zakulowa, an nunka yawan wadanda ake yi wa gwaji, ta yadda a kullum ana yi wa mutum 1,500 gwaji.

14. Mun bada horo ga Jami kiwon lafiya su 700 kuma mun tura jami’an Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa a Jihohi
19 na kasar nan.

15. Lagos da Abuja kadai a halin yanzu na da wadatar kwantar da masu dauke da cuta 1000 a cibiyoyi daban-daban.

16. Jihohi da dama sun kuma gidan cibiyoyin killace masu cuta da kulawa da su. Gwamnatin Tarayya za ta Gina wasu cibiyoyin a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa.

17. Za mu yi amfani da kudaden mu da wadanda mu ka samu ta hanyoyin gudummawa mu zuba wa wadannan cibiyoyi kayan aiki. Dama tuni mu ka zuba jami’an lafiya a wadanda mu ka rigaya mu ka gig-gina.

18. Addu’ar mu da fatan mu su ne kada Allah ya sa mu yi amfani da dukkan wadannan cibiyoyi da ake kan ginawa. Amma da dai ko ba komai, mun yi wa kan mu shirin ko-ta-kwana kenan.

19. A nan tilas na jinjina wa gagarimin ayyukan da jami’an lafiyar mu ke yi, musamman a jihohin Lagos, Ogun da kuma Abuja (FCT).

20. Kun zama wasu gwarzayen da a matsayin mu na al’ummar kasa daya, ba za mu taba mantawa da gagarimar gudummawar da ku ka bayar a cikin wannan mawuyacin hali ba.

21. Najeriya mu na kan hanya madaidaiciyar da za mu yi galaba a kan cutar Coronavirus.

22. Sai dai kuma har yanzu ina cikin damuwa dangane da karin yawaitar masu kamuwa da cutar da kuma wadanda ta ke kashewa da fadin duniya da kuma musamman a nan kasar.

24. Ya zuwa ranar 30 Ga Maris, ranar da mu ka fara kafa dokar killace kai a gida, yawan wadanda suka kamu da cutar a duniya ya haura mutum 780,000.

24. Amma zuwa yawan wadanda suka kamu da cutar a duniya ya haura mutum milyan 1,750,000 a cikin makonni biyu.

25. Wadanda cutar ta kashe a cikin makonni biyu sun haura mutum 70,000.

26. A cikin wadannan kwanakin dai har ila yau, mun ga yadda wannan cuta sha kan manyan kasaahe mafi karfi da kasaita ta kowane fanni a duniya.

27. Mu a nan Najeriya a ranar 30 Ga Maris, 2020, mutum 131 ne ke dauke da cutar, sannan ya zuwa wannan rana ta kashe mutum biyu.

28. Amma zuwa safiyar yau mutum 328 me suka kamu, kuma ta kashe mutum 10.

29. Za mu bayar da fifikon sa kaimi a jihar Lagos da sauran daidaikun wuraren da cutar ta fi saurin yaduwa.

30. Akasarin wadanda suka kamu da cutar a Lagos da Abuja duk mutanen da suka yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje. Sai kuma wadanda suka kamu da cutar daga su wadanda suka kamu da ita daga kasashen waje din.

31. Rufe filayen jiragen sama da kan iyakokin kasar nan da iyakokin ruwa ya hana tunkudo cutar ta kan iyakokin mu. Amma kuma abin mamaki, yawan wadanda ke kamuwa da cutar a cikin kasa na kasa tayar mana da hankali.

32. Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta shaida min cewa ana yawan samun masu kamuwa da cutar a cikin garuruwa. Saboda haka tilas mu tashi tsaye mu hana ta yaduwa ta hanyar kamuwa daga mutum zuwa wani mutum.

33. A wannan lokaci zan kara umartar jama’a su kara yin kaffa-kaffa wajen kauce wa daukar wannan cuta, ta hangar daina cakuda da jama’a, matakan tsafta da kuma zaunawa a gida.

34. A kan haka na sa hannu kan sabuwar dokar killace mutane saboda Coronavirus, wadda za a fito da bayanan da ta kunsa dalla-dalla, ba da dadewa ba.

35. Kwarin guiwar da mu ke samu daga jama’a ya ta’allaka ne da karfi da kokarin da mu ke yi mu na zakulowa da yin gwaji tare da killace masu dauke da wannan cuta.

36. A yau, manyan hanyoyin kauce wa kamuwa da wannan cuta su ne hana zirga-zirga barkatai, yin nesa-nesa da jama’a, sai kuma haramta taron dimbin jama’a a gwamutsu a wuri daya. Saboda haka idan aka ci gaba a haka, to za mu dakile yaduwar wannan cuta.

37. Matakan da mu ke bi su ne kare rayukan ‘yan Najeriya da ba sauran mazauna kasar nan. Da kuma kare rayuwan ma’aikatan mu da na ‘yan kasuwar mu.

38. A kan wadannan dalilai ne, tare kuma cewa bayan mun yi nazarin rahoton Kwamitin Shugaban Kasa Mai Hana Yaduwar Coronavirus, mu ga babu wata dabara, sai dai mu kara tsawaita dokar hana zirga-zirga a jihohin Lagos, Ogun da Abuja (FCT), tsawon wasu kwanaki 14, tun daga Litinin, 11.59, daidai da yau 13 Ga Afrilu, 2020.

39. Wannan cuta ba fa abin dauka da wasa ba ce, ko dai mu tashi mu dakile ta, ko kuma ta kashe mu. An kulle Masallatan Ka’aba da ke Makka da Masallacin Madina. Paparoma ya hudubar Easter shi kadai, ba tare da halartar dimbin masu saurare ba a Dandalin St. Peter Square. Mutanen da suka halarci taron Easter a mashahuriyar Hasumiyar Notre Dame, ba su wuce su goma ba. An kulle kasashen Indiya, Italia da Faransa. Wasu kasashen duk sun dauki wannan mataki. To mu ma ba za a bar mu a baya ba.

40. Dukkan wadanda aka yi wa uzirin yin zirga-zirga a waccan doka ta farko, a yanzu ma an sake yi musu.

41. Wannan mataki ne mawuyaci da mu ka dauka, amma ina da yakinin cewa shi ne matakin da yacdi dacewa. Saboda akwai hujjojin muhimmancin daukar wannan mataki a bayyane.

42. Mun san akwai fuskantar manyan kalubalen kuncin da al’umma za su fuskanta kafin karshen wannan dokar ci haga da zaman gida.

42. Tilas kada mu bari nasarar da muka samu a baya ta zama koma-baya. Tilas kada mu bari wannan cuta ta ci gaba da yaduwa a cikin jama’a. Mu daure mu kara bada goyon baya zuwa nan gaba kadan, ba da dadewa ba.

44. Ina kira da ku gaggauta kiran jami’an da abin ya shafa idan ku ko wasu na ku su ka kamu da wasu alamomin da ke nuni cewa sagwangwaman cutar Coronavirus ne.

45. Ina sane da irin yadda wannan dokar za ta shafi masu kananan karfi, musamman ‘yan tireda, masu aikin neman na cin yau da na gobe, masu sana’o’in hannu sa sauran su.

46. Su ba’arin irin wadannan masu sana’o’i, cin su da shan su ya dogara ne kacokan tilas sai sun fita daga gida sannan za su samu. Sun dogara ne da cakuduwa da gwamutsuwa cikin rintsin jama’a. Amma duk da haka, wannan ba zai sa mu sauya dokokin da muka tsaurara ba.

47. Za mu ci gaba da ayyukan raba kudade da abinci da rangwamen dakatar da biyan bashi a wannan lokacin kamar yadda mu ka yi a baya.

48. Na kuma bada umarni a kara yawan magidantan da ake bai wa tallafi daga milyan 2.6 zuwa milyan 3.6 nan da makonni biyu.

49. Tashin da jami’an tsaro su ka yi haikan wajen fuskantar wannan kalubale abin alfahari ne da su. Ina kara jinjina a gare su, tare da yin kira su ci gaba da aikin su haikan wajen sa-ido da kuma tabbatar da cewa an bi doka.

50. Ya ku ‘yan Najeriya, ina kira ku bi Ka’idojin da aka gindaya a kan daina shiga rintsin jama’a da yin nesa-nesa da juna. Shirme ko tanargazar da wasu ‘yan kalilan za su tabka, ta na iya janyo rasa rayukan dimbin jama’a. ‘Yancin ka bai ce ka danne ‘yancin wasu ba.

51. A yadda Gwamnonin Jihohi ke daukar matakai abin a yaba musu ne, musamman inda suka dauki matakan da suka yi daidai da irin na Gwamnatin Tarayya.

52. Cikin makonnin nan masu zuwa Kwamitin Shugaban Kasa Mai Hana Yaduwar Cutar Coronavirus zai ci gaba da taimakawa da ba ku goyon baya.

53. Tilas na gode wa Majalisar Tarayya dangane da hadin kai, goyon baya da gudummawar da suka bayar a wannan mawuyacin hali.

54.Kamar yadda mu ka sani, gaba daya duniyar ta canja, sakamakon wannan annoba. Yadda mu ke mu’amala da juna, harkokin hada-jada, kasuwancin da tafiye-tafiye duk sun canja.

55. Domin Tabbatar da cewa tattalin arziki mu ya saisaita a kan halin da duniya ke ciki, na umarci Ministocin Harkokin Masana’antu, Cinikayya da Zuba Jari, Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, Sufuri, Sufurin Jirage, Cikin Gida, Kiwon Lafiya, Ayyuka da Gidaje, Kwadago da na Ilmi su zauna su fito mana cikakken sabon tsarin “Tattalin Arzikin Najariya da za a yi aiki da shi a lokacin gaganiyar yaki da cutar Coronavirus”.

56. Wadannan Ministoci za su samu taimakawa ne daga Kwamitocin Bunkasa Tattalin Arziki na Shugaban Kasa wajen aiwatar da wannan gagarimin aiki.

57. Ina kuma umartar Ministan Harkokin Noma, Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Tsaro, Mataimakin Shugaban Hukumar Samar da Abinci ta Kasa da Shugaban Kwamitin Samar da Takin Zamani Na Shugaban Kasa su zauna to tabbatar da cewa sun yi iyakar kokarin su wajen rage illar da cutar Coronavirus za ta yi wa shirin noma a wannan damina mai zuwa.

58. A karshe ina godiya ga Kwamistin Hana Yaduwar Coronavirus na Shugaban Kasa, bisa namijin kokarin da su ke yi.

59. Ya ku ‘yan Najeriya, ba na tantama cewa idan mu ka ci gaba da aiki tare da junan mu, cikin bin ka’idojin da aka gindaya, za mu iya dakile wannan cuts kuma mu sake mikewa tsaye kyam da karfin mu garau.

60. Ina godiya dangane da juriyar sauraren jawabi na da ku ka yi. Allah ya albarkaci Najeriya.

Share.

game da Author