Gwamnatin Jihar Barno ta yi karin haske kan mutuwar da wani majiyyaci ya yi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, har abin ya kai ga jama’a sun shiga firgicin zargin cutar Coronavirus ce ta kashe shi.
Mataimakin Gwamnan Barno, Umar Kadafur, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yaki da Cutar Coronavirus ta Barno, ya gana da manema labarai, inda ya shaida musu cewa har yanzu ba a gano takamaimen musabbabin rasuwar mamacin ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka dauko majiyyacin daga garin Gwoza, inda ya ke aiki a karkashin wata kungiyar sa-kai, zuwa Asibitin Koyarwar Jami’ar Maiduguri, inda ya mutu a can.
Amma kuma jami’an lafiya a asibitin sun bayyana cewa cutar da ta kashe mamacin ta na da sagwangwamai iri daya da Coronavirus.
Mataimakin Gwamna Kadafur ya ce an debi samfarin jikin mamacin an tura gwaji. Kuma tuni aka tura da sakamakon ga Hukumar NCDC, wadda ya ke da alhakin bayyana yadda sakamakon gwajin ya ke.
Kadafur ya ce ya na da kyau ya ja hankalin kafafen yada labarai dangane da yayata cewa mutumin wai akwai alamun cutar Coronavirus a jikin sa.
Ya kara da cewa idan har an samu bayanin sakamakon da NCDC, to zai yi wa manema labarai jawabi.
“Ba daidai ba ne wanda ba ya da ikon yin gwaji ya gano cuta kawai ya yi kintacen wai wani na dauke da cutar, alhali ba auna shi aka yi, aka samu cutar a jikin sa ba.”
Har yau dai ba a samu mai cutar ko daya a Maiduguri ba.