Wata fitacciyar mai kula da harkokin farfajiyar fina-finan Hausa a Najeriya, Hassana Dalhat, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa farfajiyar na bukatar taimakon gaggawa musamman a yanzu da ala muran farfajiyar ke dada tabarbarewa.
Hassana Dalhatu ta bayyana haka ne a hira da ta yi ranar Lahadi a Kaduna da wakilin PREMIUM TIMES.
” Abinda ya fi tada min da hanakali shine yadda abubuwa ke dada tabarbarewa a farfajiyar fina-finan Hausa, musamman ta abin da ya shafi cinikayya samun abin yi.
” Tunda aka maida fim sai a sinima za a rika haskawa mutane da dama suka fada cikin matsala a sana’ar so musamman ‘yan kasuwa. Idan ka tafi kasuwannin mu yanzu wasu da dama sun rufe shaguna. Babu kasuwa yanzu kwata-kwata. Saboda dama a harkar saida fim ne suka samun abinci.
” Babu yadda su kansu masu yin fim din za su yi saboda, matsalar masu satar fasaha. Sun koka da yadda masu satar fasaha ke saka su suyi hasarar gaske. Dole ya zamo su koma sinima ko za su tsira daga ayyukan wadannan bata gari.
” Ku duba yadda Rahama Sadau ta rika tallata fim dinta ‘Mati A zazzau’ saboda ko da a Sinima din ba a samun yadda ake so. Dole ne dai sai ana dawo an sake duba yadda za a ceto masana’antar ta yadda zai amfani kowa da kowa. Hakan shinme mafita.
Hassana ta ce babbar hanyar da za a bi kuwa shine idan gwamnati ta saka hannu tsundum a ciki. Ta taimakawa farfajiyar. Sannan kuma masu hannu da shuni suma su saka hannu tananan ne za a samu ci gaba.
” Gwamnatocin arewacin kasar nan za zasu iya amfani da wannan fanni na nishadantarwa domin sama wa matasan yankin ayyukan yi. Akwai ayyuka da dama da matasa zasu iyayi su tsaya da kafafun su a harkar fim, ada kuma ana more haka amma yanzu komai ya durkushe.