Dalla-Dalla: Halin da Coronavirus ta jefa duniya a lokacin hutun Easter

0

An gudanar da Easter a cikin halin zaman zullumi, rudani, makoki da kuma zaman killace kai a cikin gidaje a yawancin kasashen duniya.

Bukin Easter ya zo ne a daidai lokacin da Coronavirus ta taso al’ummar duniya da kisan da musan shekaru 100 ba a ga irin wannan mummunar annoba ba.

Nazarin bayanan da PREMIUM TIMES ta tattara daga kasashe daban-daban ya nuna yadda cutar Coronavirus ke raguwa a wasu kasashen, a wasu kuma a lokacin ne ta ke musu rubdugun kisa.

Cutar Coronavirus ta kama fiye da mutum milyan tare da kashe sama da mutum 95,000 a duniya.

NAJERIYA: Zuwa ranar Lahadi mutum 323 ya kamu da cutar, amma an tanbatar da 45 sun warke har an sallame su daga killacewar da aka yi musu a cikin mako daya. Hakan ya sa jimillar wadanda suka warke sun kai 85. Amma kuma ta kashe mutum 10 a Najeriya, ya zuwa karfe 9:30 na Daren Lahadi.

SPANIYA: An samu ragowar yawan masu kamuwa da cutar da kuma yawan wadanda cutar ke kashewa a kullum.

Wadanda suka kamu a cikin makon nan zuwa ranar Lahadi ba su fi kashi 2.6% ba, idan aka kwatanta da kashi 12% a kasrshen Maris da kuma kashi 20 a tsakiyar Maris.

Zuwa ranar Lahadi, wadanda cutar ta kashe a Spain sun kai adadin mutum 16, 997, yayin da wadanda suka kamu da cutar kuma su ka karu daga 161,852 zuwa 166,019 a ranar Lahadi.

PAPAROMA: Babban Limamin Cocin Katolika na duniya, Paparoma ya gudanar da hudubar sa ta ranar Lahadin Easter a katafaren cocin da ke fadar sa, ba tare da dimbin Kiristoci sun halarta ba, kamar yadda aka saba kowace shekara.

A wannan shekara, jama’a kalilan ne aka gayyata, su ma sun zauna nesa da junan su, bisa bin ka’idar kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus.

A hudubar ta sa, wadda kacokan ta kare ne a kan cutar Coronavirus, ya gargadi Tarayyar Turai cewa an idan kasashen yankin na su tashi sun taimaki juna ba magance cutar, to kowace za ta ci karo da kuncin wahala a gaba.

AFRIKA TA KUDU: Zuwa ranar Lahadi wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Afrika ta Kudu, su 2, 173 ne. Sannan kuma jami’an lafiyar kasar sun tabbatar da cewa mutum 25 ne cutar ta kashe.

LIBYA; ‘Yan tawaye mabiya dan tawaye Khalifa Haftar sun kai mummunan hari da makami mai linzami a wani asibitin da ake kula da masu cutar Coronavirus a Tripoli, babban birnin kasar.

Gwamnatin Hadin Guiwar da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita (GNA), ta tabbatar da kai wannan halo da aka yi, kuma ta ce a yanzu dai mutum 25 kadai ke dauke da cutar a Libya, kuma ta kashe mutum daya tilo.

FARANSA: Wadanda cutar Coronavirus ta kashe a kasar Faransa sun karu a ranar Lahadi, daga mutum 13, 832 zuwa 14,393.

Zuwa ranar Lahadi Coronavirus ta kama mutum 95,403 a kasar Faransa.

TURKIYYA: Ma’aikatar Lafiyar Turkiyya ta ce mutum 1,101ne cutar Coronavirus ta kashe a kasar, kuma mutum 56,956 suka kamu da cutar zuwa yammacin Lahadi.

Hakan na nufin cikin awa 24 an samu karin mutum 4789 sun kamu kenan.

CANADA: Zuwa ranar Lahadi da dare, jami’an lafiya sun kididdige mutum 23, 919 ne suka kamu da cutar, kuma daga cikin su ta kashe mutum 674.

SRILANKA: An gudanar da zanga-zanga a bangaren musulman kasar, wadanda suka nuna rashin amincewar su a rika kone gawar wanda cutar Coronavirus ta kashe.

Gwamnatin Srilanka ce ta sa wannan doka, su kuma musulman kasar suka ki amincewa, har suka yi zanga-zanga, bayan kone gawarwakin mutum 7 da cutar ta kashe, wadanda uku daga cikin su musulmai ne.

KORIYA TA AREWA: Koriya ta Arewa ta kara tashi tsaye haikan wajen aikin gwaji da kuma tsaurara matakan haka Coronavirus shiga kasar. Har yau dai babu labarin bullar cutar a can.

ISRA’ILA: Jami’an tsaro sun killace unguwar Yahudawa masu ra’ayin rikau da ke Bnei Braie kusa da Tel Avev.

Share.

game da Author