Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce dole sai ma’aikata sun nuna tausayi da sanin yakamata kan halin kunci da annobar COVID-19 ta saka mutane ta hanyar agaza musu, in ba haka ba wahalar zai yi yawa matuka.
El-Rufai ya yi bayanin haka ne da Kara wayar da Kan mutane game da wannan shiri a tattaunawa da yayi da gidajen yada labaran jihar a Kaduna ranar Talata.
Gwamna El-Rufai ya ce da ma’aikatan gwamnati, da yan siyasa masu bada shawara, duk basu wuce mutum 100,000 ba a jihar. Amma kuma mutanen Kaduna sun kusa miliyan 10. Dole sai mu masu karbar albashin muna ganganda mun taimaka musu.
” Ko addinin mu ma ya bada dama da horon mu, mu rika taimakawa wadanda basu da shi. Dalilin haka yasa na ce dukkan mu zamu dan tsakuri wani abu daga albashin mu mu taimaka wa marasa karfi a jihar.
” Gwamnatin Kaduna ta umarci duka manyan ma’aikatan ta, da ya hada da kwamishinoni, Manyan Sakatarori, masu ba gwamna Shawara, shugabannin ma’aikatu su ba da gudunmawar naira 500,000 a wannan watan Afrilu. Sannan za su rika bada rabin Albashin su duk wata har sai an bude gari.
Ma’aikatan gwamnati dake karbar albashin naira 67,000 duk wata za su rika bada kashi 25% na albasin su duk wata har sai an bude gari. Babu wani ma’aikaci da zai rasa kasa da naira 50,000, da zai rika maneji har zuwa a bude gari.
A karshe ya ce gwamnati ta yi haka ne da manufa mai kyau ba don ta muzguna was wani ma’aikaci ba.
Sai dai kuma gamayyar kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu mallakan jihar JUTIKS, ta koka kan zaftare wani kaso daga albashin su da gwamnati ta yi.
Kungiyar wadda ta fitar da wata takarda domin haka ta ce suma albashin na su bai ishe su ba ballantana kuma ace za a zaftare wani abu a ciki.
Sun ce yin haka muzguna musu ne da nuna karfin iko kawai.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Noah Danlami da sakataren kungiyoyin Jubrin Makamai da suka saka hannu a takardar sun ce lallai da sake, domin sun amince ta hanyar kungiyar Kwadago su bada Kashi biyar ne daga albashin su, sai kwatsa suka ji gwamnati ta yanke wannan shawarar zaftare Kashi 25% na albashin su.
El-Rufa’i ya ce gwamnati bata da matsala wajen biyan albashin ma’aikata domin ita ce jihar da ta fara bayan ma’aikata da sabuwan tsarin mafi kankantan albashin ma’aikata.
Sannan kuma ta kara kudin fansho da ake biyan tsoffin ma’aikatan jihar.
Discussion about this post