Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya koka kan yadda dakunan ajiye gawa suka cika fam a Legas.
Gwamnan ya ce dole sai an rage gawarwakin mutane a dakunan ajiye gawa a asibitocin da suke jihar domin samun wurin da za ajiye wadanda suka rasu.
Saidai ya ce ba wadanda suka rasu bane daga cutar coronavirus ya sa wuraren suka cika, ya ce gawarwakin mutanen da suka rasu ba a bizne su bane saboda dokar hana walwala da aka saka.
Ya ce daga yanzu gwamnati ta bada damar wadanda za su bizne gawar wani nasu dake ajiye su je asibitoci su dauka su bizne su.
Sai dai yace an gindaya sharudda da dole za a bi a lokacin da za a bizne gawar Kamar haka:
1 – Kada mutane su wuce 20 da za su raka gawar zuwa makabarta harda Fastocin da za aje da su.
2 – Dole a yi nesa-nesa da juna a lokacin bizne kawar.
3 – Duk wadanda za su halarci bukin bizne gawar sai sun saka takunkumin fuska da safar hannu, kuma su wanke hannayen su idan suka dawo gida.
4 – Babu buki kwata-kwata da akan yi wajen kai gawa ko kuma idan an dawo.
A karshe ya jaddada cewa mutum 20 ne kawai suka mutu daga Coronavirus a jihar Legas saboda haka kada mutane su yi zaton wai wadan da suka kamu da coronavirus ne.
Discussion about this post